--
Gwamnonin da EFCC ke bincike kan rashawa a Najeriya sun ƙaru, in ji Abdulrasheed Bawa

Gwamnonin da EFCC ke bincike kan rashawa a Najeriya sun ƙaru, in ji Abdulrasheed Bawa

>





 Gwamnonin da EFCC ke bincike kan rashawa a Najeriya sun ƙaru, in ji Abdulrasheed Bawa


Shugaban hukumar EFCC da ke yaƙi da rashawa, Abdulrasheed Bawa ya ce bijiro da batun sauya fasalin kuɗi a Najeriya na taimaka musu wajen yaƙi da rashawa, kuma hanya ce ta farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.


Bawa ya kuma shaida cewa adadin gwamonin da ake bincike kan zargi haramta kuɗaɗen haramu sun karu daga mutum uku da suka bayyana a baya.


Sai dai kuma Bawa yaƙi bayyana su waye gwamnonin da kuma yawansu.


Ya kuma shaida cewa hukumar ICPC ta kuma kwato naira biliyan 117 tsakanin Janairu zuwa Agustan 2022.


Sannan ya kuma ce akwai kuɗaɗen ƙasar da CBN har yanzu ba ta san inda suka shiga ba, don haka wannan wata dama ce ta kwato kudaden kasar da kuma karya wadanda suka wawushe dukiyar kasar.

SOURCE 👇

Mikiya Hausa Labarai 24 on Facebook. 

0 Response to "Gwamnonin da EFCC ke bincike kan rashawa a Najeriya sun ƙaru, in ji Abdulrasheed Bawa"

Post a Comment