Gwamnatin Tarayya ta fara bada hutun haihuwa na kwanaki 14 ga iyaye maza da ke aikin gwamnati a Najeriya.
Tuesday, 29 November 2022
Comment
Gwamnatin Tarayya ta fara bada hutun haihuwa na kwanaki 14 ga iyaye maza da ke aikin gwamnati a Najeriya.
Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Dr. Folasade Yemi-Esan, ta bayyana haka ne a ranar Litinin a wata takarda mai lamba HCSF/SPSO/ODD/NCE/RR/650309/3, mai kwanan wata 25 ga Nuwamba, 2022.
Miss Folasade tace: "Sau ɗaya za a ba da wannan hutun a cikin shekaru biyu
kuma ga iyakar yara hudu".
Ta ce hakan ya yi dai-dai da tanade-tanaden dokokin aikin gwamnati, bugun 2021.
Wannan dai hutu ne domin iyaye mazu samu damar shakuwa da jariran su.
Idan za a iya tunawa, a watan Yunin 2018, gwamnatin ta kara hutun haihuwa ga iyaye mata daga watanni uku zuwa hudu.
source /credit /Rahama Radio on Facebook.
0 Response to "Gwamnatin Tarayya ta fara bada hutun haihuwa na kwanaki 14 ga iyaye maza da ke aikin gwamnati a Najeriya."
Post a Comment