EFCC ta ƙwace gidaje 40 na Sanata Ekweremedu.
IMAGE SOURCE :BBCHAUSA FACEBOOK
Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta samu umarnin kotu don ƙwace gidaje da gine-ginen Sanata Ike Ekweremedu 40 na wani lokaci.
Mai shari'a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Abuja ne ya sahale wa EFCC buƙatar ƙwace gidajen na tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa a ranar Juma'a cikin ƙarar da ta shigar tana neman ƙwace su don gudanar da bincike kan su.
Hukumar na zargin sanatan da mallakar kadarorin "ta haramtattun hanyoyi kamar halasta kuɗin haram".
Hotunan gidajen da EFCC ta wallafa sun ƙunshi na Abuja da kuma Jihar Enugu, inda nan ce jihar sanatan ta asali.
Yanzu haka Ekweremadu na fuskantar shari'a a birnin Landan game da tuhumar yunƙurin cire sassan jikin wani matashi da kuma yin safararsa zuwa Birtaniya ba bisa ƙa'ida ba.
An kama sanatan da matarsa a watan Yunin da ya gabata a Landan bisa zargin kai wani mai suna David Nwamini da zimmar cirar ƙodarsa don bai wa 'yarsu maras lafiya.
NEWS SOURCE :BBCHAUSA FACEBOOK
0 Response to "EFCC ta ƙwace gidaje 40 na Sanata Ekweremedu."
Post a Comment