Duk Talaucinka in kana da mata ta gari, jinka zaka yi kamar kafi kowa kudi da Sarauta a duniya.
Image source /credit /Facebook
Duk Talaucinka in kana da mata ta gari, jinka zaka yi kamar kafi kowa kudi da Sarauta a duniya.
Wannan maganar haka take wallahi bisa wadannan Dalilan 👇👇👇👇
Duk yadda kake tunanin babu to Indai matarka ta gari ce to babu maganar yawan bukatu, kai idan kace yakamata ayi wannan ayi wancan wallahi zata ce aa abarshi.
Duk kokarin da kayi kace ga wannan ammafa bashi da yawa zata ce to Allah yasamu dace kuma Allah ya kawo babban rabo.
Mace ta gari wallahi duniya ce saboda zaka iyya shekara guda bakayi mata dinki ba kuma ko damuwa bazatai ba wallahi.
Mace ta gari akwai tsoron Allah da yawan ibada bata wasa da hakkin mijinta, kai wallahi ko kayanka ka ajiye zata kula dasu
Zata dinga mutum ta ka da iyayen ka da yan uwanka.
Idan matarka ta gari ce koda zakai mata Kishiya wallahi zata iyya taimaka maka da shawarar da zakayi amfani da ita,
Dadai sauransu, sai dai kawai muci gaba da adduar Allah ya kyauta rayuwar mu duniya da lahira amin thumma amin.
0 Response to "Duk Talaucinka in kana da mata ta gari, jinka zaka yi kamar kafi kowa kudi da Sarauta a duniya. "
Post a Comment