Duk duniya ba wanda ya fi ƴan Nijeriya kai ƙara kotu, Alƙalin Alƙalai ya koka
Image source /credit /Daily Nigerian Hausa on Facebook.
Duk duniya ba wanda ya fi ƴan Nijeriya kai ƙara kotu, Alƙalin Alƙalai ya koka
Alkalin Alkalan na Ƙasa, CJN, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, ya yi ƙorafin cewa ƴan Nijeriya, musamman ƴan siyasa su ne suka fi kowa kai ƙara kotu, inda hakan ke wahalar da ɓangaren shari'a.
Mai shari’a Ariwoola ya bayyana hakan ne a yau Litinin a Abuja, a wajen taro na musamman na kotun koli da aka gudanar don bikin shiga shekarar shari’a ta 2022/2023 da kuma rantsar da sabbin manyan lauyoyi 62 na Nijeriya, SAN.
A cewar CJN, a duk ‘yar rashin jituwa, sai mu garzaya kotu, kuma a duk shari’ar da ba mu samu nasara ba, sai mu garzaya kotun daukaka kara har zuwa Kotun Koli, komai kankantar taƙaddama.
“Hakan ya haifar da cunkoson kararraki da dama da ke gaban Kotun Koli.
"Duk da cewa muna shan suka daga jama'a game da yawan tuhume-tuhume, amma ba mu da iko a kan shari'o'i da ke zuwa kotu ko kuma ba mu da ikon da za mu iya kaiwa ga kowa da kowa.
"Mun sha maimaita cewa yawancin kararrakin ya kamata a bar su a kawo karshen su a kotun daukaka kara, amma har yanzu ba a aiwatar da irin wannan tanadin kundin tsarin mulki don haka ba mu da wani laifi."
Ya ce yana da kyau a yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima a dakatar da kararrakin da ake yi a gaban kotun koli kuma ya kamata a kawo karshen irin wannan kara a kotun daukaka kara.
Source /credit /Daily Nigerian Hausa on Facebook.
0 Response to "Duk duniya ba wanda ya fi ƴan Nijeriya kai ƙara kotu, Alƙalin Alƙalai ya koka"
Post a Comment