Duba da wadannan halayan Gaskiya rayuwar Mawaki rarara abar koyi ce wallahi
Rayuwar Mawaki Rarara Tana Burge Ni Musamman Yadda Yake Taimakon Abokanan Sana'arsa, Iyayensa Da 'Yan Uwansa
Daga Comr Abba Sani Pantami
A bangaren mu na marubuta 'yan "Media" da suka samu madafun iko, Allah ya ba su dama babu mai taimakon abokanan aikin shi da zaka kwatan tashi da mawaki Dauda Rarara.
Duk yadda baka son Dauda Rarara ko don bambancin jam'iyya ko wani abu makamancin haka baka isa ka kushehi akan rashin taimakon abokanan aikin shi ba, haka iyayen shi da iyayen abokanan shi da 'yan uwan shi 'yan garin su da sauran mutane, shiyasa duk yadda makiyan shi suka sako shi a gaba basu iya samun Nasara akan shi saboda taimakon da yake yi.
A bangaren mu na marubuta 'yan kalilan ne wa 'yanda suka samu madafun iko masu taimakawa na kasa dasu, hassada da rowa da bakin ciki ne suka jawo hakan, amma da suna taimakon na kasa da su da ba haka ba.
Duk gwamnonin Najeriya da manya da kananan 'yan siyasa babu wanda bai damu da social media ba tare da bata muhimmanci, shiyasa kowane dan siyasa yana da manyan wakilai da yake nadawa a bangaren media saboda muhimmancin da take dashi a wurin shi.
Amma mukarraban dake jagorantar media din sune suke kudun dune komai su cinye ba tare da suna taimakon na kasa dasu ba, hatta taimako da dan siyasa zai yiwa 'yan media a karkashin su ake yi amma sai su hana ruwa gudu ko su karbi kudin su cinye ko kuma su hana a taimaki na kasa dasu din.
Source 👇
Rariya on Facebook.
0 Response to "Duba da wadannan halayan Gaskiya rayuwar Mawaki rarara abar koyi ce wallahi "
Post a Comment