--
 Dalar Amurka Da Ke Ƙa sa Da 2021 Za Ta Dena Aiki A Watan Janairu 2023 - Gwamnatin Amurka.

Dalar Amurka Da Ke Ƙa sa Da 2021 Za Ta Dena Aiki A Watan Janairu 2023 - Gwamnatin Amurka.

>

 








Dalar Amurka Da Ke Ƙa sa Da 2021 Za Ta Dena Aiki A Watan Janairu 2023 - Gwamnatin Amurka.


A ci gaba da taron ban mamaki da aka kammala a birnin Washington DC a ranar 2 ga Nuwamba, 2022 tsakanin Babban Bankin Tarayya na Amurka, da kuma ofishin Kwanturolar Kuɗi, IMF, Bankin Duniya da Gwamnonin Babban Bankin Afirka, gwamnatin Amurka ta tsaida rana don dena karɓar takardar kuɗi ta Dalar Amurka wanda zai fara a ranar 31 ga Janairu, 2023.


Taƙaddamar na nuna cewa duk wata takardar dalar Amurka da ke ƙa sa da 2021 da aka buga ba za ta ƙara samun karɓuwa ba.


Wannan na zuwa domin daƙile masu ayyukan ta'addanci, garkuwa da mutane, da gurɓatattun ƴan siyasa da manyan ɓarayin gwamnati. 


A matsayin wani ɓangare na aiwatar da tsauraran shirin, za a ba wa bankunan tsakiya na Afirka aiki tare da wakili na musamman daga ofishin kwanturolar kuɗi, da mai gudanarwa na babban bankin ƙasar Amurka don bincikar duk wani shige da fice da dala keyi.


Rahoton ya kuma bayyana cewa, shugaban na Amurka ya kuma rubutawa gwamnatin Birtaniya da kungiyar Tarayyar Turai da su tsaya a layi ɗaya tare da sa ke fasalin kuɗaɗen su yadda ya kamata domin daƙile waɗanda ke da kuɗaɗen da ba su samu ba a dalar ta Amurka.


Daga Aliyu Tsiga


Source : arewa post on Facebook. 

0 Response to " Dalar Amurka Da Ke Ƙa sa Da 2021 Za Ta Dena Aiki A Watan Janairu 2023 - Gwamnatin Amurka."

Post a Comment