DA DUMI-DUMI: An Min Cushen Naira Biliyan 206, A Kasafin Kuɗin Ma'aikata Ta Na 2023, Cewar Sadiya Farooq
Tuesday, 22 November 2022
Comment
DA DUMI-DUMI: An Min Cushen Naira Biliyan 206, A Kasafin Kuɗin Ma'aikata Ta Na 2023, Cewar Sadiya Farooq
Ministar ma'aikatar jin-ƙai a Najeriya ta yi zargin cewa an yi mata cushen naira biliyan 206 a kasafin kuɗin ma'aikatarta.
Ministan jinkai sadiya umar farooq tana zargin wasu dayi mata cushe a kasafin kudin na Ma'aikatan ta kamar yadda ta bayyana a lokacin zaman kwamitin kula da ayyuka na musamman na majalisar dattawan Nigeria a jiya litinin.
Haka zalika Sadiya Farouk ta kara da cewa zata nisanta kanta da wannan kudin kimanin Naira bilyan 206, da aka cusa a kasafin kuɗin ma'aikatar ta na wannan shekara ta 2023.
Me zaku ce?
~ Jimina Hausa
Source 👉 Hasken Shiriya on Facebook.
0 Response to "DA DUMI-DUMI: An Min Cushen Naira Biliyan 206, A Kasafin Kuɗin Ma'aikata Ta Na 2023, Cewar Sadiya Farooq "
Post a Comment