Babu tashin hankalin da ya wuce auren dole ga ya mace
Image source /credit/Facebook.
Auren dole ya kasance wani babban alamarine dayake ciwa mata tuwo a kwarya. Ita dai wannan al ada tsohuwa ce a cikin alummar Hausawa kuma haryanzu tana cigaba ta faruwa kamar wutar daji.
Illar auren dole đđđ
Yana haddasa kisan kai, ansha samun Rahotanni na kisan kan da auren dole ya hadda sa. Yazama dole AKula akwai hadari,
Yana haddasa kin amanar aure:
Ansha samun korafin zinace zinace akan auren dole, wasu matan basa hakuri suna bin tsofaffin samarin su hartakai suna lalata dasu duk saboda auren dole.
Yana haddasa yawan zawarawa :,
Yawancin zawarawa sunbada hujjoji akan auren dole ne yasa suka gudo daga gidajen mazajensu.
Yana kawo Bijirewa iyyaye,
Yana haddasa hawan jini/haifar da rashin lafiyar jiki.
Wannan atakaice kenan, maganar gaskiya yakamata ace wannan alamarin yazama tarihi a kasar Hausa, saboda ko da addini nin musulunci yayi hani dashi kuma aladama tayi hani dashi.
0 Response to "Babu tashin hankalin da ya wuce auren dole ga ya mace "
Post a Comment