Ba zai yiwu mu biya malaman jami'a albashin aikin da ba su yi ba - Gwamnatin Najeriya .
Image source : BBC HAUSA FACEBOOK
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta faɗi dalilin da ya sa ba ta biya mambobin ƙungiyar ASUU ta malaman jami'a cikakken albashinsu na watan Oktoba ba, tana mai cewa ba zai yiwu a biya malaman albasahin aikin da ba su yi ba.
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ɗauki matakin daina biyan albashin malaman jami'ar na tsawon lokacin da suka ɗauka suna yajin aiki tun daga 14 ga watan Fabarairu zuwa 14 ga Oktoba.
Bayan dawowarsu aikin ne kuma gwamnati ta biya su albashin kwana 17, kamar yadda ASUU ke faɗa, kuma ta yi barazanar ɗaukar mataki.
Hakan ta sa reshen ƙungiyar na Jami'ar Jos ya umarci malaman jami'ar su yi zamansu a gida, duk da cewa ta ce ba yajin aiki suke yi ba.
Cikin wata sanarwa, mai magana da yawun Ma'aikatar Ƙwadago, Olajide Oshundun, ya musanta rahotannin da ke cewa gwamnati ba ta yi wa malaman adalci ba.
"An biya su kuɗin aikin da suka yi ne kawai a Oktoba, daga ranar da suka soke yajin aiki," a cewar sanarwar.
"An ɗauki matakin ne saboda ba zai yiwu a biya su kuɗin aikin da ba su yi ba. Kowa ta kansa yake yi."
SOURCE :BBCHAUSA FACEBOOK
0 Response to "Ba zai yiwu mu biya malaman jami'a albashin aikin da ba su yi ba - Gwamnatin Najeriya . "
Post a Comment