--
An sanya Liverpool a kasuwa

An sanya Liverpool a kasuwa

>

 



 Fenway Sports Group (FSG), mamallakan kungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool FC, sun sanya kungiyar ta gasar premier ta Ingila a kasuwa .


Kamfanin ya shirya gabatar da ƙungiyar ga masu sha'awar saye, kuma yana aiki tare da Goldman Sachs da Morgan Stanley don su yi masa dillanci.


Rahotanni sun ce yanke shawarar siyar da kungiyar na zuwa ne watanni bayan an sayar da kungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea kan kudi fan biliyan 4.25.


Kamfanin wasanni na Amurka ya sayi Liverpool FC daga George Gillett da Tom Hicks a cikin watan Oktoba, 2010.


Tun daga watan Mayu 2022, Forbes ta yiwa Liverpool farashi na dala biliyan 4.45 (£ 3.89 biliyan). Amma tare da aka sayar da Chelsea ga LA Dodgers Todd Boehly kan fam biliyan 4.25 a farkon wannan shekara, ƙungiyar ta Merseyside na iya buƙatar wannan farashin daidai da yadda a ka sayi Chelsea.


A baya dai FSG ta samu tayi daga wasu kamfanoni uku wadanda suka nuna sha'awarsu ta zuba hannun jari a Liverpool. 


Kamfanin ya ce a koyaushe kofa a bude ta ke ga wadannan tayin kuma a shirye ya ke ya yi la'akari da su, idan aka yi la'akari da sharuddan da suka dace.


Source :daily nigerian Hausa Facebook. 

0 Response to "An sanya Liverpool a kasuwa"

Post a Comment