Ƴan sanda sun saki tinkiyar da su ka tsare bisa laifin cinye soyayyen kifi a Borno
IMAGE SOURCE : DAILY NIGERIAN HAUSA
Rundunar ƴan sanda ta jihar Borno ta saki wata tinkiya da aka kama da laifin cinye soyayyen kifi da wani Malam Yusuf Ibrahim ke sayar wa a unguwar Bulabulin, Maiduguri, babban birnin jihar.
Jaridar Zagazola Makama ta rawait ran Ibrahim ya ɓaci a jiya Asabar bayan da tinkiyar ta kuma zagayo wa, ta faki idanun Ibrahim ta daka wa kifin wawa, har da dangwalar yaji, ta kuma tsere abin ta.
Mai kifin ya yi ƙorafin cewa watanni 5 kenan tinkiyar, mallakar wata mai suna Luba Mohammed, tana cinye masa magana sana'ar sa, shi ne ya nemi ƴan sanda da su kamo ta domin hukunci.
Mai sayar da kifin ya koka da kakkausar murya kan cewa tunkiyar da ke unguwarsu ɗaya, ta haifar masa da asara har jarin sa ma na shirin karye wa.
Sai dai bayan da tunkiya ta kai wa kifinsa hari a ranar Asabar, daga karshe ya yanke shawarar shigar da ‘yan sanda.
Daga baya ‘yan sanda sun kama tunkiya kuma suka tsare ta cikin dare.
Daga bisani hedikwatar ‘yan sanda ta Bulabulin ta sake shi a ranar Lahadi bayan da Ibrahim ya sasanta da mai shi.
Daga karshe dai Ibrahim ya hakura ne bayan da manyan unguwa su ka haɗu su ka ba shi hakuri, inda duk da haka sai da ya shinfida sharuɗɗan cewa idan ta nuna to zai shigar da kara.
SOURCE :DAILY NIGERIAN HAUSA
0 Response to "Ƴan sanda sun saki tinkiyar da su ka tsare bisa laifin cinye soyayyen kifi a Borno"
Post a Comment