An sacewa wani ango wayoyi guda biyu, bayan an ɗagashi sama a ranar Aurensa.
Sunday, 6 November 2022
Comment
Image source : Jaridar arewa Facebook
An silalewa Ango wayoyi har guda biyu, a lokacin da abokansa suka dagashi sama, bayan kammala daurin aurensa. Angon Mai suna Musa wanda aka daura aurensa da amaryarsa Amina, a ranar Alhamis, a garin Gezawa da ke jihar Kano.
Lamarin ya sanya Angon cikin damuwa da jimami, kamar yadda na hannun damansa yake bayyawa Jaridar Arewa. Inda yace lafiya lau da wayoyinsa aka kammala daurin aurensa, amma bayan an dagashi sama, sai ya laluba ya ji wayam.
Rahotannin sun nuna cewa har kawo yanzu ana buga lambar wayar anki dagawa, daga karshe ma sun kashe wayar, wanda hakan na nufin basa da niyar dawowa da ita ga mamallakinta.
Daga karshe dai angon yace “Ga duk wanda Allah yasa ya ganta ko yaji duriyarta, to ya garzaya koda layin ne ya maidoman, ya rike wayar idan ita yake bukata” Inji Angon ya shaidawa abokinsa.
Source :Jaridar arewa Facebook
0 Response to "An sacewa wani ango wayoyi guda biyu, bayan an ɗagashi sama a ranar Aurensa."
Post a Comment