--
An kama direbobi ƴan ƙasashen waje da ke satar mai a Nijeriya

An kama direbobi ƴan ƙasashen waje da ke satar mai a Nijeriya

>

 



Wasu ma’aikatan manyan tankokin mai 16 ƴan asalin kasashen ketare sun gurfana gaban wata Kotu dake jihar Rivers a tarayyar Najeriya bisa zargin su da hannu a safarar danyen mai daga Najeriyar ba bisa ka’ida ba.


Rfi ta rawaito cewa wannan sabon al’amari dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Najeriya ke kokarin dakile yawan satar danyen mai da ke faruwa a kasar, abin da ke janyowa kasar asarar biliyoyin daloli.


Mahukuntan Nijeriya sun zargi mutanen da dibar mai a gabar ruwan Akpo ba bisa ka’ida ba tun a watan Agustan da ya gabata, kuma dakarun rundunar sojin ruwan kasar suka kama su da kuma tankar man.


A karin bayanin da ta yi rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce an cafke tankar man ne a Equatorial Guinea bayan da mahukuntan kasar suka tsare ta, tare da sanar da jami’an Najeriya.


Wadanda ake zargin da dukannin su ma’aikatan jirgin ne sun musanta laifin da ake tuhumar su da aikatawa, sai dai duk da haka mai shari’a Turaki Muhammad ya bada Umarnin tsare su karkashin ikon rundunar sojin ruwan kafin a tattaro wasu karin mutane 10 da ake zargin su tare.


Bayanai sun tabbatar da cewa mutanen sun hadar da ‘yan asalin kasashen India, Sri Lanka da Philiphines.


SOURCE 👇

DAILY NIGERIAN HAUSA ON FACEBOOK. 

0 Response to "An kama direbobi ƴan ƙasashen waje da ke satar mai a Nijeriya"

Post a Comment