--
Ƴan jam'iyyar NNPP sun yi al'ajabin dandazon al'umma da su ka tarbi Kwankwaso a Cross River

Ƴan jam'iyyar NNPP sun yi al'ajabin dandazon al'umma da su ka tarbi Kwankwaso a Cross River

>









Magoya bayan jam’iyyar NNPP, a yau Asabar, sun bayyana ziyarar da ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya kai Cross River a matsayin wacce babu kamar ta a jihar.


Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, dandazon magoya baya ne su ka yi tsinke a yayin da Kwankwaso ya buɗe ofisoshin yakin neman zabe guda biyar a Cross River.



Ofisoshin yakin neman zaben da ya buɗe sun haɗa da na Sanata Sam Eno a Ugep, karamar hukumar Yakuur da na Wilfred Bonse, hedkwatar shiyyar Sanatan Cross River ta tsakiya, Ikom.


Sauran sun hada da hedikwatar yakin neman zaben Yakubu Shandam, mazabar tarayya ta Boki Ikom, na Sanata Caroline Williams, Ogoja, Sanata ta Cross River na Arewa da Yakubu Shandam Campaign Office Okondi, Katame, Karamar hukumar Boki Local, ofishin kamfen na BenClay Campaign Office, Okondi Boki 1 State Constiturter.


Bangaren ‘yan jam’iyyar da ‘yan takarar da suka zanta da NAN bayan kaddamarwar sun bayyana cewa kaunarsa ga ci gaban kasa ta kara daukaka jam’iyyar a jihar.


Buba Galadima, sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar, ya bayyana cewa ziyarar tasu ta zama iri daya ce kuma shi a wajensa dawo wa gida ce a gare shi, ya kara da cewa tawagar shugaban kasa ta samu kyakkyawar tarba daga al’ummar Cross River.


“Hakika wannan ziyarar maimai ce. Rabo na da saka kafa kamar a Ikom, Ogoja da sauran wurare shi ne a shekarar 1972 lokacin ina dalibi a jami’a.


SOURCE :   Daily Nigerian Hausa Facebook. 

0 Response to "Ƴan jam'iyyar NNPP sun yi al'ajabin dandazon al'umma da su ka tarbi Kwankwaso a Cross River"

Post a Comment