A kowace rana za'a dinga fitar da ganga dubu 120 na danyen man fetur dake jihar Gombe da Bauchi.
A kowace rana za'a dinga fitar da ganga dubu 120 na danyen man fetur dake jihar Gombe da Bauchi.
Da kuma kubik miliyan 500 na iskar gas kowace rana a yankin, abin da zai kai ga samar da hasken wutar lantarki mai karfin megawatt 300 da kuma kamfanin samar da takin zamanin da zai rika samar da tan dubu 2 da 500 kowace rana.
A yau shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da rijiyoyin man Fetur guda biyu wanda suka zama sune na farko a tarihin yankin Arewa, wannan babban aikin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar babban abun a yaba mishi ne.
Jihar Gombe da Bauchi sun zama daya daga cikin jihohin Najeriya da kuma afrika da suke da arzkin man Fetur.
Duk wanda yake tunanin wannan man Fetur din bazai amfani talaka ba, to tabbas bai fahimci alfanu dake tattare dashi ba, kafun mu fara rubutu akai yana da kyau kowa ya bincika yaga yadda jihohin dake da arzikin man Fetur suka kasance wurin cigaba da samun kudaden shiga tare da wasu Alkhairai masu yawa.
Wannan aikin shine rukunin farko akwai rukuni na biyu da za'a kammala, kuma Insha'Allah bazai dade ba. Muna Godiya Baba Buhari.
Daga Comr Abba Sani Pantami
Source 👇
Fitila Hausa on Facebook.
0 Response to " A kowace rana za'a dinga fitar da ganga dubu 120 na danyen man fetur dake jihar Gombe da Bauchi."
Post a Comment