--
Zaben 2023 :Tinibu Yagana Da Yan Fim Din Hausa Inda Ya Basu Naira Million 50 Aziyarar Da Ya Kai Jihar Kano

Zaben 2023 :Tinibu Yagana Da Yan Fim Din Hausa Inda Ya Basu Naira Million 50 Aziyarar Da Ya Kai Jihar Kano

>

 






ZABEN 2023: Tinubu Ya Gana Da 'Yan Fim Din Hausa, Inda Ya Ba Su Naira Milyan 50, A Yayin Ziyarar Da Ya Kai Jihar Kano, Amma Ya Ki Ganawa Da Marubutansa Masu Tallata Shi A Kafafun Sadarwa, Kuma Ya Ki Ba Su Ko Kobo


Daga Comr Abba Sani Pantami


A kusan kowane lokaci idan muka yi magana akan irin haka sai mutane suke ganin kamar muna yiwa 'yan Kannywood da mawaka hassada ne ko kuma muna nuna muma kwadayayyune amma abun ba haka bane, wallahi aikin da marubuta masu tallatar dan siyasa suke mishi yafi tasiri da amfani sama da duk abunda 'yan Kannywood zasu mishi. 



Saboda marubuci shine mutum na farko da yake fara tallata dan siyasa duniya tasan shi a cikin kankanin lokaci, marubuci shine mutun na farko da yake fara nunawa al-ummah Alkhairan ka, marubuci shine mutum na farko da yake fara bawa dan siyasa kariya a cikin kankanin lokaci kan duk wani kalubale da ya tunkaro dan siyasa, marubuci shine mutum na farko da yake fara bawa dan siyasa gudummuwa fiye da yadda ake tunani kafun sauran al-umma musamman a wannan karnin da muke ciki.



Ba muce 'yan Kannywood ko mawaka basu bada gudummuwa ba dukkanmu munga hakan kuma munsan da haka, amma marubuci shine gaba da kowa har shi kanshi mawakin marubuci ne yake taimaka masa ta fannoni da dama.


Ya kamata mu marubuta mu kara sanin darajar kanmu da mutuncin kan mu, idan ba haka ba, babu wani cigaba da zamu samu balle wani dan siyasa ya dinga kallonmu da mutunci da kima.




Atiku da Tinubu duk basu san kima da darajar marubutan dake amfani da kafofin sada zumunta ba, amma na tabbata wata ran zasu sani kuma nan bada dadewa ba, domin alkalami yafi takobi kaifi.

0 Response to "Zaben 2023 :Tinibu Yagana Da Yan Fim Din Hausa Inda Ya Basu Naira Million 50 Aziyarar Da Ya Kai Jihar Kano "

Post a Comment