--
SENATE PRESIDENT AHMAD LAWAN YA KOKA KAN HANA YAN MAJALISUN TARAYYAR NIGERIA HUKUNTA MASU LAIFUKAN RASHAWA

SENATE PRESIDENT AHMAD LAWAN YA KOKA KAN HANA YAN MAJALISUN TARAYYAR NIGERIA HUKUNTA MASU LAIFUKAN RASHAWA

>





Image source : daily Nigeria. 

Ga raayin Ahmad lawan akan cin hanci da rashawa 👇👇

Ahmed Lawan ya nuna damuwa kan rashin ikon majalisun tarayya su riƙa hukunta laifin cin-hanci


Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan a yau Litinin ya nuna damuwa kan rashin iko da majalisun tarayya ke da shi a yaki da cin hanci da rashawa da kuma wawure dukiyoyin al'umma sabo da kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999 ya yi wa ƴan majalisu katanga wajen aiwatar da hukunci kan lamarin.


Lawan ya fadi haka ne da ya ke sharhi a kan wata maƙala da tsohon Kakakin majalisar wakilai, Demeji Bankole ya gabatar a yayin bikin yaye dalibai karo na 6 na Cibiyar Koyar da Ilimin tafiyar da Mulki da Dimokuraɗiyya ta Ƙasa ta Jami'ar Benin, da a ka gudanar a majalisar tarayya.


Lawan ya ce sashe na 88 na kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya baiwa majalisar tarayya ikon fallasa wanda ya aikata cin hanci da rashawa da kuma wawure dukiyar al'umma, amma bai bada ikon yin hukunci ba.


"Gaskiya ita ce , kundin tsarin mulkin ƙasana 1999 da akai wa kwaskwarima ya tauye ikon ƴan majalisu. Sashe na 88 ya bada damar ƴan majalisa su fallasa cin hanci da yin barna da dukiyar ƙasa sai ya tsaya a nan.


"Sabo da haka idan ka fallasa laifi kuma baka da ikon yin hukunci to ya za ai hakan ya kawo gyaran matsalolin?


"Kamar da a ce ka ga ɓarawo ne, sai dai kawai ka ce "ɓarawo ɓarawo, ole!!  amma ba za ka iya zama ɗan sanda ka kama ɓarawon ko kai shi ƙara ba. Gaskiya an gurgunta majalisa, wannan gaskiyar magana kenan," in ji shi

0 Response to "SENATE PRESIDENT AHMAD LAWAN YA KOKA KAN HANA YAN MAJALISUN TARAYYAR NIGERIA HUKUNTA MASU LAIFUKAN RASHAWA"

Post a Comment