--
Gwamnatin Nijeriya ta soki shirin sake fasalin Naira da CBN ke ƙoƙarin yi

Gwamnatin Nijeriya ta soki shirin sake fasalin Naira da CBN ke ƙoƙarin yi

>







 Image source :Facebook 


Sa'o'i 48 bayan Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa bankin zai sauya fasalin kudin kasar a ranar 15 ga watan Disamba, 2022, gwamnatin tarayya ta ki amincewa da shirin a yau Juma'a.


 Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare ta Kasa, Zainab Ahmad, wadda ta yi watsi da batun shirin, ta ce idan aka aiwatar da shi to zai yi illa ga kasa da tattalin arzikinta.


Zainab, wacce ta yi tsokaci kan manufar yayin da ta ke amsa tambayar da Sanata Opeyemi Bamidele ya yi, yayin zaman kare na kasafin kudin 2023, ta gargadi CBN kan sakamakon da ka iya tasowa daga gare ta.


Sanata Bamidele wanda a cikin tambayarsa ya shaida wa Ministar Kudi cewa kwanaki biyu bayan sanarwar da CBN ya fitar, an fara jin tasirin hakan kan darajar Naira zuwa Dalar Amurka, ya ce, “Kwana biyu kacal da sanar manufar, darajar Naira zuwa Dalar Amurka ta tashi daga N740 zuwa N788 zuwa dalar Amurka sakamakon gaggawar musayar Naira zuwa kudaden kasashen waje, musamman dala.


"A gare ni, manufar na iya zama kyakkyawan tunani, amma lokacin aiwatar da ita ne bai yi ba duba da cewa hakan zai zubar da darajar Naira zuwa har N1,000 a kan dalar Amurka kafin ranar 31 ga Janairu, 2023 don aiwatar da manufar gabaɗaya.."


Yayin da take amsa tambayar, ministar ta ce ba ta da masaniya kan manufar, inda ta ƙara da cewa a kafafen yada labarai kawai ta ji sanarwar.


Ta ce, “Ya ku Sanatoci masu girma , ba a tuntube mu a ma’aikatar kudi da CBN ya yi ba game da shirin sake fasalin Naira kuma ba za mu iya cewa komai dangane da cancanta ko akasin haka ba .


"Duk da haka a matsayi na ta ƴar Nijeriya da ke da damar kasancewa a kan gaba a harkokin kasafin kudin Najeriya, manufar da aka fitar a wannan lokaci, tana nuna mummunan sakamako kan darajar Naira ga sauran kudaden waje.


“Duk da haka, zan yi kira ga wannan kwamiti da ya gayyaci gwamnan babban bankin na CBN domin samun cikakken bayani game da cancantar manufofin da aka tsara da kuma daidai ko akasin haka na aiwatar da shi a yanzu.

0 Response to "Gwamnatin Nijeriya ta soki shirin sake fasalin Naira da CBN ke ƙoƙarin yi"

Post a Comment