--
Gwamnati ta ɗau hanyar fitar da ƴan ƙasa miliyan 100 daga talauci – Minista

Gwamnati ta ɗau hanyar fitar da ƴan ƙasa miliyan 100 daga talauci – Minista

>



Image source :FACEBOOK 

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, ya ce gwamnatin tarayya na daf da samar da ayyukan yi na din-din-din ga ƴan ƙasa miliyan 21 tare da fitar da mutane miliyan 35 daga kangin talauci nan da shekarar 2025.
Sambo, a cikin wata sanarwa da kakakin sa, Sam Idiagbonya, ya fitar, ya bayyana hakan a jiya Juma’a a taron bita na ministoci na 2022 da ke gudana a Uyo, Akwa Ibom.
A cewarsa, fannin sufurin na kan Gwadabe na cimma kudurin gwamnati na fitar da ƴan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci a cikin shekaru 10.


“Wannan shine don saka hannun jari mai yawa a kan ababen more rayuwa, tabbatar daidaito a fannin kananan sana’o’i, inganta yanayin saka hannun jari, inganta yanayin rayuwa da aiwatar da dakile sauyin yanayi.
“Wannan zai samar da ayyukan yi na din-din-din har miliyan 21 da kuma fitar da mutane miliyan 35 daga kangin talauci nan da shekarar 2025, ta yadda za a kafa hanyar cimma kudurin gwamnati na fitar da ƴan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10.
“Shirye-shiryen suna da nufin bunƙasa harkar sufuri a ƙasar nan tare da dabarun hangen nesa na matsakaicin lokaci.
“Na san cewa dukkan ku kuna sane da waɗannan manyan manufofin, saboda sun zama tsarin bin diddigin aiwatar da ayyukanmu,” in ji Sambo.

SOURCE :DAILY NIGERIAN HAUSA. 

0 Response to "Gwamnati ta ɗau hanyar fitar da ƴan ƙasa miliyan 100 daga talauci – Minista"

Post a Comment