--
 Wata Sabuwa! Ba mu da masaniyar CBN zai sauya fasalin wasu takardun kudi – Zainab Ahmad Ministar kudi.

Wata Sabuwa! Ba mu da masaniyar CBN zai sauya fasalin wasu takardun kudi – Zainab Ahmad Ministar kudi.

>





Image source : DLC HAUSA


Babu wanda ya sanar da mu za a sauya fasalin kudin Nijeriya – Zainab Ahmad

Ministar kudin Nijeriya Zainab Shamsuna Ahmad ta ce babban bankin kasar CBN bai tuntubi ma’aikatar da take jagoranta ba wajen kokarin sake fasalta wasu takardun kudin Nijeriya.

Ministar ta furta haka ne a lokacin wata muhawara kan kasafin kudin ma’aikatar a Abuja.

Ministar ta ce duk da dai babban dalilin wannan matakin shi ne na a shawo kan matsalar hauhawar farashin kaya, sai dai ta tabbatar da cewa dole akwai bi-baya.

Zainab Ahmad ta ce babu wanda ya tuntube mu, kawai dai mun ji sanarwa ne kamar yadda kowa ya ji.

👇👇





0 Response to " Wata Sabuwa! Ba mu da masaniyar CBN zai sauya fasalin wasu takardun kudi – Zainab Ahmad Ministar kudi. "

Post a Comment