2023: Za mu haɗa kai da INEC don dakile sayen ƙuri’u – EFCC
Image source :daily nigerian Hausa,
2023: Za mu haɗa kai da INEC don dakile sayen ƙuri’u – EFCC
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, ta ce za ta ci gaba da hada kai da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, domin dakile ta'adar sayen kuri’u, musamman a lokacin babban zaben 2023.
Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Abuja a yau Alhamis, jim kadan bayan kare kasafin kudin hukumar na 2023 a gaban kwamitin majalisar dattawa kan yaki da cin hanci da rashawa.
"Za mu ci gaba da yin abin da ya kamata mu yi, muna kokarin tabbatar da cewa kudaden haramun ba sa samun damar shiga harkokin zaɓenmu," in ji shi.
Bawa ya ce hukumar za ta haɗa kai da INEC don kama wa tare da gurfanar da wadanda ke da hannu wajen sayen kuri’u.
Shugaban hukumar ya ce ana ci gaba da shari'ar wadanda aka kama da laifin sayen kuri'u a zabukan da suka gabata a gaban kotu.
Bawa ya kuma godewa majalisar dokokin kasar bisa goyon bayan hukumar, ta hanyar wasu muhimman dokoki da aka tsara domin kara taimaka mata wajen gudanar da ayyukanta.
0 Response to "2023: Za mu haɗa kai da INEC don dakile sayen ƙuri’u – EFCC"
Post a Comment