--
Yanzu yanzu: yadda zaman Shari'ar Abduljabbar keguda a kotu yanzu haka, Kubiyo yanzu domin samun cikakken rahoton yadda zaman yake gudana yanzu

Yanzu yanzu: yadda zaman Shari'ar Abduljabbar keguda a kotu yanzu haka, Kubiyo yanzu domin samun cikakken rahoton yadda zaman yake gudana yanzu

>


Azaman kotun na yau, Mai Shari’ah Alkali Ibrahim Sarki Yola ya fara da sauraron Shari’ar Sheikh Abduljabbar wadda Gomnatin Jihar Kano ƙarƙashin Mulkin Gwamna Abdullahi Ganduje ta shigar da ƙara kimanin watanni 11 da suka gabata.


Kamar kullum, lauyoyin ko wanne ɓangare ( masu gabatar da ƙara da masu kariya) sun gabatarwa da kotu kansu inda lauya Yakubu Abdullahi yake jagorantar ɓangaren Gwabnati, lauya Ɗalhatu Shehu Usman kuma shi ne yake jagorantar ɓangaren Malan Abduljabbar a halin yanzu.


Anfara yiwa Malam Shehin Malamin tambayoyi (Cross Examination) a halin yanzu. Anyiwa Malamin kimanin tambayoyi 36, inda hakan ya sanya aka zo gaɓa wacce aka buƙaci sake sanya/kunna wancan audio daka sanya/kunna a wancan zama da ya gabata, domin jin kalmar biyan buƙata ta Ɗa Namiji wacce lauyan Gwabnati yace Malamin ya faɗeta. Shi kuma Malamin ya musanta hakan.


Bayan an kunna wannan audio ne sai guda cikin wakilin lauyoyi Gomnati, mai suna Uwaisu Al’arabi Fagge ya kunna, namfa hayaniya ta kaure a kotun, tayadda akajiyo cewa, audio da aka kunna ya sha bambam da wanda aka kunna a wancan zama. Al’amarin da yasa Alƙali dakatar da zaman kotun izuwa wani lokaci, yanzu haka ana dakon Alƙali domin ya bada umarnin a cigaba da wannan zama.

0 Response to "Yanzu yanzu: yadda zaman Shari'ar Abduljabbar keguda a kotu yanzu haka, Kubiyo yanzu domin samun cikakken rahoton yadda zaman yake gudana yanzu"

Post a Comment