Takardar da ya rubuta a yau wani ci gaba ne na cika sharuɗɗan da DSS ta ba mawaƙin, a cewar kakakin MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma cikin takardar sanarwa ga manema labarai.
Na Tuba, Ba Zan Kara Ba, Cewar Mawaƙi Sufin Zamani A Wasikar Da Ya Baiwa ‘Yan Fim Din Hausa Haƙuri
Daga Ali Kano
Mawaki Sarfilu Umar Zarewa ya ba ‘yan fim ɗin Hausa haƙuri a cikin wata takarda da ya aika masu, tare da alƙawarin ba zai ƙara ɓata masu suna ba.
Mujallar Fim ta bada labarin yadda Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Fim ta Nijeriya (MOPPAN) ta kai ƙarar Sufin Zamani wajen Hukumar Tsaron Ƙasa (DSS) saboda ɓatancin da ya yi wa mata ‘yan fim a wata waƙa, inda ya ce wai ba su son zaman aure.
Waƙar ta ɓata wa ‘yan fim da dama rai, kuma sun yi na’am da matakin da MOPPAN ta ɗauka a kan sa.
Bayan an tsare shi tsawon kwana ɗaya, aka bada belin shi, daga nan ya yi bidiyo inda ya bada haƙuri ga ‘yan fim, ya ce shi da ma cin zarafin wani ba halin sa ba ne.
Takardar da ya rubuta a yau wani ci gaba ne na cika sharuɗɗan da DSS ta ba mawaƙin, a cewar kakakin MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma cikin takardar sanarwa ga manema labarai.
A cikin takardar, mai taken “Takardar Neman Afuwa”, mawaƙin ya yi nadamar abin da ya aikata tare da bayyana tuban sa. Ya ce: “Ni Sarfilu Umar Zarewa, wanda aka fi sani da Sufin Zamani mai waƙar ”Yar Lukuta’, ina mai neman afuwar wannan ƙungiya ta MOPPAN mai albarka bisa kuskuren da na yi na yin waƙar da ta ɓata wa ‘yan masana’antar Kannywood rai.
“Allah ya sa(n) ni ban yi wannan waƙa don na ɓata wa wani ko wata rai ba. Saboda haka ina neman afuwar ku, kuma in-sha Allahu hakan ba za ta sake faruwa ba. Na gode.”
Da yake bayyana ra’ayi kan takardar ban-haƙurin, Ciroma ya ce, “Wannan shi ne tabbacin ya ɗauki dukkanin gyaran da aka yi masa.”
Sharuɗɗan da DSS ta ba Sufin Zamani dai su ne:
1. Zai yi bidiyo da odiyo na ban-haƙuri da kuma ƙaryata kan sa game da waƙar ɓatancin da ya yi.
Karanta kuma Hotunan bikin Lilin Baba da Ummi Rahab (1)
2. Zai yi waƙa kishiyar wacce ya yi, wato ya yabi matan Kannywood, ya faɗi alherin su kuma ya nuna masu zaman aure ne.
3. Zai rubuta wa MOPPAN takardar ban-haƙuri.
4. Zai yi wa hukumar alƙawari a rubuce, wato ‘undertaking’, cewar ba zai ƙara yin ɓatanci ga duk wani ɗan fim ba.
5. Bayan ya yi wannan kuma hukumar DSS za ta yi masa hukuncin da ya dace, domin ya yi musu ƙarya a farkon kamun da aka yi masa.
A yanzu dai ya cika sharuɗɗa uku, wato na 1 da na 2 da kuma na 3.
0 Response to "Takardar da ya rubuta a yau wani ci gaba ne na cika sharuɗɗan da DSS ta ba mawaƙin, a cewar kakakin MOPPAN na ƙasa, Malam Al-Amin Ciroma cikin takardar sanarwa ga manema labarai."
Post a Comment