Labari da Dumi-Dumin kan Kisan Hanifa--Ban san yadda a kai Hanifa ta mutu ba -- Tanko
Ban san yadda a kai Hanifa ta mutu ba -- Tanko
Abdulmalik Tanko, mai makarantar da a ke zargi da kashe Hanifa Abubakar, ya ce shi da sauran mutane biyu da a ke tuhuma ba su san yadda a ka yi yarinyar, ƴar shekara 5 da haihuwa ta rasu ba.
Tanko ya baiyana haka ne a jiya Litinin yayin da ya ke kare kan sa a gaban babbar kotu a Jihar Kano.
A na tuhumar Tanko mai shekara 34 tare da Hashimu ɗan shekaru 37 da kuma Fatima Musa mai shekara 26, dukkan su mazauna Tudun Murtala a gaban babbar Kotun.
A na tuhumar su da laifuka 5 da su ka haɗa da yunƙurin garkuwa da mutum, garkuwa da mutum, haɗin baki, ɓoye gawar Hanifa da taimaka wa a aikata laifin.
A wata shaida da M.L.Usman ya jagoranta, lauyan da ke kare shi, Tanko ya ce shi da mutum biyun da ake tuhuma ba su san yadda marigayiya Hanifa ta rasu ba.
Ya ce a cikin watan Disambar 2021, ya samu matsala ta kudi sosai, don haka ya je banki neman lamuni, amma aka ce masa bai cika sharuɗɗan bayar da irin wannan lamuni ba.
“A ranar 4 ga Disambar 2021, na yanke shawarar in je in ɗauko Hanifa a makarantar Islamiyya a adaidaita sahu, na dauke ta, na kai ta gidana da ke Tudun Murtala a Kano.
" Da na isa gida, matata ta tambaye ni ƴar wane ne, na ce mata ƴar ɗaya daga cikin ma’aikatana ce da ta yi tafiya, kuma nan da kwana biyu zuwa uku za ta dawo.
“A ranar 10 ga Disamba, 2021, ina kan hanyara ta zuwa kasuwa sai na haɗu da wani Habu, wanda ya nemi aikin gadi a makaranta ta amma har yanzu ba a ɗauke shi aiki ba.
“Na ce masa ina da aiki mai sauki da zan bashi sabo da haka ya zo makarantar da ke Tudun Murtala; Na ce masa akwai yarinyar da zai kula mini da ita na kwana ɗaya kacal a cikin harabar makarantar.
"Sai mu ka yi musayar lambar waya kuma ya yarda ya zo da misalin karfe 11:30 na dare, daga nan muka rabu.
“A wannan ranar da misalin karfe 10:00 na dare na ɗauke Hanifa da ga gida na a lokacin da take barci mai nauyi; nisan gidana zuwa makaranta bai yi nisa ba.
"Hanifa ta kwana a daya daga cikin ofisoshin makarantar a kan kujera kuma na kulle na bar ta a makarantar," in ji Tanko.
Ya kuma shaida cewar a hanyarsa ta komawa gida ya yi kokarin kiran Habu ɗin, inda ya ƙara da cewa washegari da misalin karfe 7:30 na safe ya je makarantar, sai ya kaɗu da ganin Hanifa ta na barci kamar yadda ya bar ta.
“Na taɓa hannunta amma ba ta motsa ba,” in ji shi, inda ya shaida wa kotun cewa ya yi wa wanda ake kara na biyu ƙarya da ya zo ya binne gawar da ya ɓoye ta a cikin buhu a harabar makarantarsa.
A yayin tuhumar, lauyan masu shigar da ƙara, Antoni-Janar na Jihar Kano, Barr. Musa Abdullahi-Lawan, ya tambayi wanda ake kara ko wadanda ake kara na biyu da na uku sun san an sace Hanifa da kuma yadda ta mutu daga baya.
Tanko ya amsa cewa su biyun ba su da masaniyar cewa an yi garkuwa da marigayiyar da kuma yanayin da ya kai ga mutuwar ta.
Alkalin kotun, Mai shari’a Usman Na’abba, ya ɗage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 10 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron kariya.
Laifukan da ake tuhumar su Tanko sun saɓa da sashe na 97, 95 da 273, 274(b) da 277 na kundin laifuffuka na dokokin jihar Kano, 1991.
0 Response to "Labari da Dumi-Dumin kan Kisan Hanifa--Ban san yadda a kai Hanifa ta mutu ba -- Tanko"
Post a Comment