Yanzu-Yanzu | Saudiyya Ta sanar da ganin Watan Ramadan:- Cikakken Bayanin kan Guzirin Masu Azumi.
Guzirin Watan Ramadan
Marubuci :- Mahmud Isah Yola
Cikin ta ana buɗe ƙofofin Aljannah don
masu shiga, ana kulle ƙofofin wuta Saboda
ba’a fatan a samu masu shiga.
Shaiɗanu masu umurtan mutane da
miyagun ayyuka an ɗaɗɗaure, ko wani
dare Allah yana ‘Yanta dubban bayi ya
musu kyautar Aljannah ya kuma amintar
dasu daga Wuta , a cikin ta akwai wani
dare, da ibada a cikin shi yana dai-dai da
ibadan shekara tamanin da ‘Yan Kai.
Ya kai Mai fatar rahamar ubangijinsa ,
yawaita ayyukan alkahairai cikin wata
domin samun yardan ubangijinka.
Ya kai mai aikata saɓo ko laifi, ka sani ya
wajaba a kanka ka bari cikin wannan
wata , in har ko ka ƙi, tsinuwan Manzon
Allah (S.A.W) ta tabbata a kanka, duk
wanda annabi ya tsine masa kuwa ya
halaka.
Wani al’amari na musamman:
Allah ta’ala na cewa:
”Lallai mun saukar da wannan Kur’ani
cikin dare mai albarka………. A cikin ta ake
rarrabe dukkan al’amari…”
Suratud Dukhan.
Wannan aya Malaman tafsiri sukace:
Tana nuna cikin Ramadan ake ƙaddara
abubuwan da zasu auku ga bayi a shekara,
na alkhairi ko sharri.
Saboda haka ka dukufa wajen addu’an
Allah ya sada ka da alkhairan da kake
buƙata, ya kuma kare ka daga sharrin da
kake tsoro.
Addu’ar mai azumi karɓaɓɓiya ce.
Kenan za’a baka alkhairan da ka nema , a
kuma kare ka sharrin da ka nemi tsari
daga gare shi.
Ya Allah ka sada mu da alkhairan wannan
wata , ka kare mu dukkan sharri, ka kuma
buga mana hatimin ‘Yan aljannah Amin.
Copied👇
UUsman Adam AhmadAUsman Adam AhmadAUsman Adam Ahmad
0 Response to "Yanzu-Yanzu | Saudiyya Ta sanar da ganin Watan Ramadan:- Cikakken Bayanin kan Guzirin Masu Azumi."
Post a Comment