--
Sanata Kwankwaso ya yi karin haske a kan ainihin dalilin da ya sa dole ya bar tafiyar PDP

Sanata Kwankwaso ya yi karin haske a kan ainihin dalilin da ya sa dole ya bar tafiyar PDP

>



Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana asalin abin da ya yi sanadiyyar ficewarsa daga jam’iyyar PDP Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya ce sabani aka samu tsakaninsa da wasu shugabannin PDP Rikicin kujerun shiyyoyi shi ne abin da ya tunzura jagoran na Kwankwasiyya har ya shiga NNPP

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi bayanin abin da ya sa ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP. Jaridar Daily Trust ta ce Rabiu Musa Kwankwaso ya shaidawa manema labarai hikimarsa na yin watsi da jam’iyyar da ya nemi takarar Najeriya a 2019.

Da yake zantawa da ‘yan jarida, Kwankwaso ya ce kimanin watanni 11 da suka wuce aka bijiro da maganar kujerun shugabannin shiyyoyi a jam’iyya. Tsohon Sanatan ya ce an warewa kowace jihar Arewa maso yamma kujerar da za ta rike, amma sai aka hana mutanensa wannan dama a jiharsa ta Kano.

wannan ya sa Kwankwaso ya ga tamkar bai da amfani a PDP.

Bayan shafe tsawon lokaci ba tare da an yi sulhu ba, ya ce sai ya sauya-sheka.

Abin da Kwankwaso ya fada 

“An samu wani yanayi a Afrilun bara inda aka raba mukamai na shiyyoyi tsakanin jihohi shida, inda aka ba mu damar mu kawo ‘yan takara.” “Amma a jihar Kano sai wasu suka ga cewa ba ni da muhimmanci, sai suka yi abin da suka yi.”

“Wannan ne ya jawo wannan lamarin (na sauya-sheka), kuma sai da na shafe shekara kusan daya kenan ina jiran jam’iyyar PDP ta zauna da ni.” “Har aka nada sababbin shugabannin jam’iyya, amma ba su da sha’awar su yi zama da ni.”

“A kan wannan dalili, na ga akwai sabanin da ba za a iya shawo kan shi ba tsakanin ni da sauran shugabannin da ake da su saboda bambancin akida.”

Na shigo NNPP yanzu - Kwankwaso 

“Yanzu na karbi katin zama ‘dan jam’iyya, kuma babu shakka ni ne sabon shiga NNPP. Ina matukar farin ciki da na zama ‘dan NNPP a Kano.”

Rabiu Kwankwaso ya shiga hangen takarar shugaban kasa da kyau, ya burma kwandon NNPP jim kadan da barin Jam’iyyar PDP. A yau ne ake sa rai jam’iyyar NNPP da Kwankwaso ya shiga za ta yi zaben shugabanni na kasa a shirin fitar da wanda zai yi mata takara a zaben 2023


Source: Legit.ng

0 Response to "Sanata Kwankwaso ya yi karin haske a kan ainihin dalilin da ya sa dole ya bar tafiyar PDP"

Post a Comment