Ramadan 2022: Wane kasashe ne Musulmai za su kwashe awanni da yawa da awanni kaɗan a Azumin bana
Ramadan 2022: Wane kasashe ne Musulmai za su kwashe awanni da yawa da awanni kaɗan a Azumin bana
Musulmai zasu fara azumin watan Ramadana a farkon watan Afrilu na wannan shekarar kuma Biliyoyin mutane ne zasu kame daga ci ko sha ko kusantar iyali na tsawon awannin rana har wata ɗaya. Watan mai tarin ni'ima da gafarar Allah SWT, zai soma yayin da wasu sassan duniya ke cikin tsawon rana, lokacin zafi, da kuma gajerun rana, lokacin sanyi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Shin kunsan wane ƙasashe ne a faɗin duniya da Musulmai za su fuskanci tsayin lokacin rana da kuma masu gajerun lokaci?
Yayin Azumin bana ƙasashen New Zealand, Paraguay, Uruguay, Argentina da kuma Afirka ta kudu ne Musulman cikinsu zasu yi gajeren Azumi da ba zai wuce awanni 11 zuwa 12. Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a! Musulman dake zaune a birnin Reykjavík, na ƙasar Iceland, sune zasu kafa tarihi a bana na kasancewar mutanen birnin da zasu yi dogon Azumi na tsawon awanni. Ana hasashen Musulman wannan birnin za su kame daga ci ko sha na tsawon awanni 16 da mintuna 50 yayin watan Azumin Ramadana na bana.
Sauran ƙasashen da ake tsammanin zasu yi dogon Azumi sun haɗa da Poland, Ingila, Faransa, Portugal, Greece, China, Amurka, da kuma Turkiyya.
Musulman dake ƙasashen da ake zuba rana tsawon lokaci ba tare da ta faɗi ba, ba zasu iya jure yin Azumi ba na tsawon awanni 20 ko fiye. Fatawowin Malamai sun nuna cewa kasashen da tsakanin faɗuwar ranar da sake fitowarta bai wuce awa uku kacal ba, suna da damar bin tsarin yadda yan uwansu na wasu biranen ke Azumi.
Mafi yawan Musulmai a irin waɗan nan ƙasashe, alal misali sukan iya bin tsarin yadda rana ke faɗuwa da fitowa a ƙasa mai tsarki wato Saudiyya. A watan Azumin bana, Saudiyya da mafi yawan kashen dake tsakiyar gabashin duniya za su yi azumi na tsawon awanni 15 kowace rana.
0 Response to "Ramadan 2022: Wane kasashe ne Musulmai za su kwashe awanni da yawa da awanni kaɗan a Azumin bana"
Post a Comment