Karon farko Sheikh Aminu Daurawa yayi magana, kan caccakar da aka yi masa
Saƙo daga Mal. Aminu Ibrahim Daurawa akan cece-kuce da ake yi a kwanakin nan.
1. Yana godiya ga Al'ummah akan amsoshi na ilimi da aka bayar, amma bai yadda da duk wani mataki na ɗaukar doka a hannu da wani zai yi ƙoƙarin zartarwa ba domin ba a gyara kuskure da kuskure, kuma shi bai kai ƙarar kowa ba.
2. Bai so yayi magana akan wannan batun ba saboda buɗe ƙofar ba da amsa a irin wannan batun zai ƙona mai lokaci, wanda shi kuma lokacinshi na nazari ne da karantarwa da sulhu da ba da gudunmawa gurin warware matsalolin Al'ummah.
3. Yana kira ga matasa da Allah ya azurta su da wayoyin hannu na zamani su sani cewa wannan wayoyin ni'ima ce babba da Allah zai tambayesu akan me suka yi da ita, don haka su yi amfani da ita gurin sauraron darussa na ilimi don inganta Imaninsu da kuma koyon hukunce-hukuncen tsarki da sallah da azumi da zamantakewa da sauran al'amuran addini.
4. Lokaci da matasa maza da mata suke bayarwa a social media ya nuna suna da wadataccen lokacin da za su iya shiga makarantun Islamiyya da zaurukan ilimi, don haka in ba su koyi ilimin addini ba to su tanadi amsar da za su bawa Allah idan suka je gurinshi ba su san addininsa ba.
5. Ɗaukar doka a hannu ya saɓawa koyarwar addinin Musulunci, don haka yana da kyau bayin Allah waɗanda Allah ya azurta su da ƙaunar addini su saita wannan ƙaunar da suke yiwa addini da koyarwar addinin.
6. Yana tunatar da Mata cewa sune ginshiƙin Al'ummah don sune suke tarbiyyantar da yara, don haka su nemi ilimin addini kuma suyi riƙo da tarbiyyar musulunci za su samu lada mai girma a gun Allah.
7. Yana kira ga duk wanda suka san cewa fannin ilimin addini ba ɓangaren kwarewarsu ba ne su daina tsoma baki a cikin al'amuran addini, domin Malamai ne suke da haƙƙin su yiwa junansu gyara in ma an samu kuskuren ba wai jahilai su tsoma baki cikin addini ba, kuma mafi girman laifi a cikin addini shine mutum ya yi magana a cikin addinin Allah da jahilci.
8. Yana tunatar da al'ummah hatsarin yankar maganar da in aka datse ta za ta canza ma'ana, wannan abu ne mai hatsari kuma yana daga cikin mafi munin ƙarya.
9. Duk wanda ya ga wata magana da yake ganin ba daidai ba ce to yayi bincike ya nemo asalin cikakkiyar maganar sannan ya turawa wasu Malamai su ya tambaye su a kai.
10. Yana kira ga Al'ummah cewa a zauna lafiya a maida hankali akan neman ilimin addini da sana'o'i, domin duk wanda bai shagaltu da abu mai amfani ba to shaiɗan zai shagaltar da shi da abu mara amfani.
A karshe yana wa dukkan Musulmi wasiyya da abun da ya zo a cikin hadisin Manzon Allah ﷺ wanda yake cewa: ka amfanu da abu biyar kafin abu biyar:
1. Samartakarka kafin tsufarka.
2. Lafiyarka kafin rashin lafiyarka.
3. Wadatarka kafin talaucinka.
4. Damar lokacinka kafin uzurirrika su rufe ka.
5. Rayuwarka kafin mutuwarka.
Ya faɗa min saƙon ne a waya, kuma bayan na rubuta abubuwan da ya faɗa na tura mishi ya kara waɗansu abubuwan.
Rubutawa: Huzaifa Aminu Daurawa
0 Response to "Karon farko Sheikh Aminu Daurawa yayi magana, kan caccakar da aka yi masa"
Post a Comment