Dubun wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi hanyar Kaduna-Abuja ya cika
Dubun wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi hanyar Kaduna-Abuja ya cika
Hukumar yan sandan ƙasar nan, ranar Alhamis, ta sanar da kame wani gawurtaccen ɗan bindiga da wasu mutum.
A wata sanarwa da rundunar yan sandan Najeriya ta fitar ranar Alhamis da yamma a Twitter, kasurgumin ɗan bindigan dan kimanin shekara 36 ya amsa cewa shi ke jagorantar tawagarsu.
"Ɗaya daga cikin waɗan da aka kama shine Ahmed Yunusa wanda suke kira Yellowa Ashana, ɗan shekara 36. Shi ke jagorantar kungiyarsu suna aikata ta'addanci a hanyar Kaduna-Abuja." "Wanda ake zargin ya amsa laifin cewa yana jagorantar tawagarsu wajen kai hari da garkuwa a hanyar, ya kuma ce sun kai hari sau uku kauyen Kadara a Kaduna, inda suka kashe mutane."
Wannan hanya ta Kaduna Zuwa Abuja ta yi kaurin suna wajen matsalar harin yan bindiga, da kuma garkuwa da matafiya, da fashi a wasu lokutan. Yan ta'addan dake yawan kai hari kan babbar hanyar mai tara dandazon matafiya, kan mamaye su, sannan su tilasta musu tsayawa. A lokuta da dama, yan ta'addan da babu tausayi a tattare da su, kan yi amfani da makamansu, su buɗe wa matafiya wuta domin tursasa su har su tsaya.
Rundunar yan sandan ƙasar nan ta bayyana cewa dakarunta sun yi ram da wani da ake zargin ƙasurgumin ɗan bindiga ne mai garkuwa da mutane, da wasu 26. Rudunar yan sanda ta ce mutanen da suka shiga hannu suna daga cikin waɗan da suka fitini mutane da kai harin garkuwa da fashi da makami, musamman a babbar hanyar Kaduna-Abuja.
0 Response to "Dubun wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi hanyar Kaduna-Abuja ya cika"
Post a Comment