--
Zamu yi amfani da karfi wajen hana zanga-zanga - Rundunar ‘yan sanda Osun

Zamu yi amfani da karfi wajen hana zanga-zanga - Rundunar ‘yan sanda Osun

>

 



Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta sha alwashin yin amfani da duk wata hanya da ta dace wajen dakile duk wata zanga-zanga ta kowace hanya, musamman a lokacin zaben gwamnan jihar dake tafe.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Wale Olokode ya ce rundunar ta samu labarin cewa wasu gungun mutane na shirin gudanar da zanga-zanga a jihar.

Da yake gargadin mutane ko gungun mutanen da ke shirin irin wannan a jihar, kwamishinan ‘yan sandan a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Yemisi Opalola, ya fitar, ya yi kira ga iyaye da su gargadi ‘ya’yansu da su guji shiga cikin munanan ayyuka a lokacin zabe.

Yayin da yake ba da tabbacin tsaro a lokacin zabukan Olokode ya sha alwashin cewa hukumomin tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tunkarar duk wani ko wasu mutane da ke yunkurin haifar da matsala tare da kawo cikas ga gudanuwarzabukan cikin tsanaki tare da tabbatar da doka.

0 Response to "Zamu yi amfani da karfi wajen hana zanga-zanga - Rundunar ‘yan sanda Osun"

Post a Comment