Sarauniyar kyau ta kashe N1.6m don ta inganta kyanta, amma fuskatar ta komaɗe bata iya murmushi
Rahotanni sun nuna cewa Likitoci sun komadar da fuskar wata sarauniyar kyau ta kasar Rasha mai suna Yulia Tarasevich, Legit.ng ta ruwaito.
A halin yanzu Yulia Tarasevich, matashiya mai shekaru 43 bata iya rufe idanuwan ta ko murmushi bayan kashe Euro 3,000 ( miliyan N1.6) don inganta kyawunta.
Hakan yasa matar mai yara biyun ta maka likitocin da suka yi mata aikin kotu, inda tayi korafi game da yadda tazo gare su da kyakyawar lafiyayyar fuska amma suka lalata.
Da alamu matar mai shekaru 43, Yulia Tarasevich ba zata sake murmushi ko rufe idanuwan ta ba, har ta kare rayuwarta.
An bar sarauniyar kyawun ta kasar Rasha da mokadaddar fuska bayan jerin aikin da aka mata don gyara tsufanta wanda ya ja mata kashe Euro 3,000 (miliyan N1.6), amma hakan bai sa sun yi nasara ba don haka ta maka likitocin da suka mata aikin kotun.
Daily Mail ta ruwaito yadda aka wa Yulia aiki a fuska, karin mazaunai da wasu ayyuka don tsatso kyau a kwayar idanuwan ta a wani asibiti a Krasnodar dake kudancin Rasha.
Sai dai, matar mai yara biyu ta lura tun bayan aikin da aka yi mata, bata iya rufe idanuwan ta ko kuma motsi da ilahirin fuskarta balle kuma murmushi.
Hakan yasa ta kara kashe karin Euro 20,000 (miliyan N11.3) don gyara mata fuskar ta zuwa daidai.
Matar mai shekaru 43 ta taba wakiltar kasar Rasha a gasar sarauniyar kyau ta duniya a shekarar 2020. Bayan kashe Euro 20,000 ( miliyan N11.3) amma hakan baisa ta yi nasara ba.
0 Response to "Sarauniyar kyau ta kashe N1.6m don ta inganta kyanta, amma fuskatar ta komaɗe bata iya murmushi"
Post a Comment