Tap di jan: EFCC ta kama Janar na bogi, duba abin da ya faru
Thursday, 13 January 2022
Comment
Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta damke wani Janar din Soja na karya kan zargin damfarar N270m (Milyan dari biyu da saba'in).
EFCC ta bayyana hakan ne a jawabin da ta saki tare da hotunan Sojan a shafinta na Tuwita
Sojan Bogin mai suna Bolarinwa Oluwasegun ya yi ikirarin cewa Shugaba Buhari ya so ya zama Shugaban hafsan Sojin Najeriya.
EFCC ta ce
Jami'ar hukumar EFCC na shiyar Legas sun damke, Bolarinawa Oluwasegun, wani Janar din Sojan karya wanda yayi ikirarin Buhari ya zabeshi matsayin Shugaban hafsan Soji da zargin damfarar N270m."
Duk yunkurin da Legit Hausa tayi na samun karin bayani daga wajen hukumar EFCCC ya ci tura.
Reported by ISYAKU.COM
0 Response to "Tap di jan: EFCC ta kama Janar na bogi, duba abin da ya faru"
Post a Comment