--
Ta faru ta kare 'Yar gwagwarmaya Fauziyya D. Suleiman ta kara bayyana Ra'ayinta Na A soke Lefe domin 'Yan Mata da Samari yawa su samu suyi aure Duba cikakken Abinda ta bayyana

Ta faru ta kare 'Yar gwagwarmaya Fauziyya D. Suleiman ta kara bayyana Ra'ayinta Na A soke Lefe domin 'Yan Mata da Samari yawa su samu suyi aure Duba cikakken Abinda ta bayyana

>


Fauziyya D. Sulaiman, na daya daga cikin fitattun marubuta labarai a Masana’antar Finafinan Hausa ta Kannywood kuma tana da gidauniya da ke tallafa wa marasa galihu mai suna Creative Helping Needy Foundation, wadda take tallafa wa marasa galihu da dama ciki har da aurar da matasa da yi musu kayan daki. 


A kwanan nan, ta fara wata yekuwar neman a samu masalaha a tsakanin ma’aurata ta yadda ba dole sai an yi lefe ko kayan daki ba. A wannan tattaunawa da Aminiya, ta bayyana dalilanta na neman yin haka:


Me ya jawo hankalinki kike ganin ya kamata a soke lefe da kayan daki?


To da farko dai ba cewa na yi kai-tsaye a soke lefe ba, cewa na yi a samu daidaito a kan harkar lefe da kayan daki. Idan misali iyaye ba su da halin da za su yi wa ’yarsu kayan daki, musamman iyaye mata, wadanda su suka fi samun matsala, a yi ta sa ranar aure ana dagawa, saboda rashin kayan daki.


Su ma daga bangaren maza, za ka ga saurayi ya fara hada kayan lefe amma ya kasa karasawa ko kuma ba ya da wurin da zai zauna, wani abu ya kakare masa, sai na ce ya kamata a samu daidaito a tsakanin iyaye.


Daga bangaren macen, idan misali an gaza hada kayan daki, musamman idan mijin bai kammala hada lefen ba, saboda ba shi da hali, ko yarinyar marainiya ce, sai a kira miji a fada masa cewa muna da matsalar kayan daki, saboda haka muna so kudin aurenta da kudin sadaki da na kayan lefe kawai a ba mu mu yi mata kayan daki.


To ka ga in aka yi haka, za a samu daidaiton da za a aurar da yara, domin akwai matsaloli da yawa na yaran da sun kai munzalin aure, amma iyayen saboda rashin kayan daki sun gaza aurar da su.


Sannan su ma samarin akwai wanda za ka ga yanayin samunsa yana da halin da zai iya rike mace, amma hada lefen a lokaci daya zai iya zame masa tashin hankali.


Shi ma abin da ya samu, wanda Allah Ya hore masa, iyayen sai su karba cikin mutunci da girmama juna. In aka yi haka, muna ganin za a samu saukin wajen aurar da ’yan mata maimakon su yi ta zama babu aure.


To yaya kike kallon wannan kira duba da yadda har auren ake fasawa a wasu wuraren saboda lefe ko kayan daki?


To, kamar yadda dama na fada, mun san abu ne da dole zai zo da kalubale, saboda wata al’ada ce da ake so a kawar ko a yi mata kwaskwarima. Duk abin da mutane suka saba da shi aka ce za a zo musu da sauyi akwai tashin hankali, sai dai idan sauyin ya zama dole ba su da yadda za su yi.


Ba kya ganin cewa idan aka karbi kudin lefe aka yi wa amarya kayan daki za ta sha gori a wajen dangin miji?


Idan har gori na dakin miji ne ai da sauki fiye da a ce tana zaune a gida tsawon shekara 25 ko 30 babu aure, wata ma tana iya fadawa wani fage na lalata.


To da wannan gorin da za a yi mata a cikin dakinta da wancan, wanne ya fi? Sai muka ce shi wancan na gidan miji ya fi sauki saboda ko ba komai tana cikin dakin mijinta, kuma ba shi mijin ne zai yi mata ba, wadansu ne daga can nesa, kuma ba ma lallai ne a yi a gabanta ba, sabanin wannan da za a zo gaban idonta a yi.


Ko kina ganin alamun nasara a wannan fafutikar?


To cikin ikon Allah, tun lokacin da muka fara maganar a kafafen sada zumunta mun ga mutane da yawa sun nuna sun karbi abin, suna ta tsokaci, suna yadawa suna cewa ya kamata.


Kuma ko mako uku zuwa hudu da suka gabata, akwai wata da aka ba mu labari, kuma mun ma gan ta, cewa iyayenta ba su da halin yi mata kayan daki, marainiya ce, sai wakilanta suka fada wa minjinta cewa da kudin sadakinta da kayan lefe komai kawai ya ba da Naira dubu 300, to da yake Allah Ya sa shi ma yana da hali ya kawo.


Daga cikin wannan kudin suka yi mata kayan daki da na sawa fitar biki. Yanzu haka tana dakin mjinta cikin rufin asirin Ubangiji.


Ko akwai wani yunkuri da kika fara yi wajen ganin mutane sun karbi wannan kira naki?


Yunkurin dai da muka fara yi da yake yawanci mu a kafafen sadarwa da na sada zumunta muka fi murya, ta nan muka fi mayar da hankali, kuma muna ganin kafafen yada labaran suna taimakawa sosai wajen yada abin.


Muna kyautata zaton insha Allahu ko da ba a samu an yi shi duka ba, to wadansu za su amsa, musamman wadanda suke cikin wannan hali na babu.


Tun farko a ganin ki, me ya kawo al’amuran aure suka ta’azzara?


To abin da ya jawo wannan matsalar gaskiya shi ne tsadar da rayuwa ta yi. A da za ka ga wani abincin gidansa ba zai gagare shi ba, amma yanzu ta kai yana gagararsa, balle a kai ga cewa za a yi kayan daki.


Sannan akwai marayun da aka mutu aka bari da yawa; a da in mutum ya mutu, dangi sukan hadu su rufa wa juna asiri, amma yanzu in dai bai mutu ya bar musu wani abu ba, to ya bar su da tashin hankali, auren ’yarsa ma sai ya nemi ya gagara.


To wadannan abubuwan sun taru sun yi yawa sosai. Kamar mu da muke da kungiyoyi masu zaman kansu, a kullum muna cin karo da irin wadannan korafekorafen.


Wata ka ga an sa ranarta sau biyar, wata an kawo kudi amma abin ya ki yiwuwa. Akwai wacce ma tsawon shekara biyar ana kawo kudi ana fasawa (na maza hudu) saboda babu. Yanzu ana na hudun ne hankalin mahaifiyarta ya tashi, ta zo tana kukan a taimaka mata, sai muka ce mata mu marasa lafiya muka fi mayar da hankali wajen taimakawa, ba masu aure ba.


To wannan ya dada tayar mana da hankali sosai wajen fahimtar halin da mutane suke ciki, tare da kiran su da su rungumi wannan shawarar.

0 Response to "Ta faru ta kare 'Yar gwagwarmaya Fauziyya D. Suleiman ta kara bayyana Ra'ayinta Na A soke Lefe domin 'Yan Mata da Samari yawa su samu suyi aure Duba cikakken Abinda ta bayyana"

Post a Comment