--
Soyayyar shan minti wanda samari da ‘yan mata suke har ma suke saduwa tana kan gaba akan mutuwar aure

Soyayyar shan minti wanda samari da ‘yan mata suke har ma suke saduwa tana kan gaba akan mutuwar aure

>


Idan akwai wani babban abin dake saurin haddasa mutuwar aure to siyayyar shan minti ita ce gaba, wanda samari da ‘yan mata suke neman junan su kafin suyi aure.

Soyayyar shan minti tana daya daga cikin abin da yake kawo mutuwar aure domin a wannan zamani da muke wannan soyayyar ta zama ruwan dare, yadda samari da ‘yam mata suke kusantar juna suna shafe-shafe ko saduwa kafin suyi aure.


Wanda hakan kuma yakan haddasa rashin zaman lafiya bayan anyi aure sakamakon rashin yarda dake shiga tsakanin ma’auratan zasuyi ta zargin junan su.


Ficacciyar marubuciyar nan mai suna Fauziyya D Sulaiman tare da shahararran malamin addinin musulinci dake jihar Kano, Sheikh Abdallah Gadon kaya.


Sunyi bayani dalla-dalla akan wadannan matsalolin dake fuskanta game da soyayyar shan minti, a vangaren Fauziyya D Sulaiman ta kawo balarin wasu ‘yam mata da zaurawa da soyayyar shan minti takai su ta baro su.


Wanda a karsge mazan da suke mu’amala da suka gudu bayan sun yaudare su sun sami abin da suke bukata a wajan matan.


A bangaren Sheikh Abdallah Gadon kaya shima ya bada labarin wasu ‘yam mata kwadayi yasa suka fada tarkon wasu maza da suka taudare su.


Wanda a karshe daya daga cikin mazan ya sadu da daya daga cikin matan wanda haf ciki ya shige ta, sannan kuma ya gudu daga gareta har ma ya sauya layin watar sa domin kada ta neme shi.

Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken bayani daga Fauziyya D Sulauman tare da Sheikh Abdallah Gadon kaya.





0 Response to "Soyayyar shan minti wanda samari da ‘yan mata suke har ma suke saduwa tana kan gaba akan mutuwar aure"

Post a Comment