--
Bayan samun yanci daga Saudiyya tayi nassarar Zama ma'aikaciyar NDLEA

Bayan samun yanci daga Saudiyya tayi nassarar Zama ma'aikaciyar NDLEA

>


Budurwa yar jihar Jigawa, Zainab Aliyu Kila wacce aka yiwa sharrin safarar kwayoyi yayinda ta tafi aikin Umrah kasar Saudiyya ta shiga hukumar yaki da kwayoyin Najeriya NDLEA.


Zaku tuna cewa a shekarar 2018, Gwamnatin Saudiyya ta daure Zainab Aliyu Kila a Kurkuku kuma ana shirin yanke mata hukunci. 


Daily Nigerian ta ruwaito cewa Zainab na cikin sabbin Jami'ai 2000 da hukumar NDLEA ta yaye a makarantarta dake Jos, jihar Plateau ranar Juma'a. Jaridar tace mahaifin Zainab, Habibu Kila ya tabbatar da hakan inda yace lallai tana da mukamin ASN yanzu.


Zainab Aliyu mai shekaru 22 da haihuwa ta tsinci kanta cikin wani maiwuyacin hali inda aka kama jakarta da miyagun kwayoyi a kasa mai tsarki. Hukuncin wannan laifi kuwa shine kisa a bisa dokokin kasar ta Saudiya. 


Bayan an dauki tsawon lokaci anata kai ruwa rana yayin bincike da kuma tattaunawa tsakanin kasashen Najeriya da Saudiya, an samun gano gaskiyar lamarin cewa ba ita keda mallakar kwayoyin ba cusa mata akayi cikin jakarta ba tareda sanin ta ba. 

0 Response to "Bayan samun yanci daga Saudiyya tayi nassarar Zama ma'aikaciyar NDLEA"

Post a Comment