Lambar (NIN) tana matsayin Rayuwarka Ne Dolene Saika Kula Sosai Ncc Tayiwa 'Yan Najeriya Gargadi Mai Zafi Duba Abinda Tace>>>
Hukumar sadarwa ta Najeriya ta aika da wani sako zuwa ga ‘yan Najeriya.
Hukumar ta bukaci ‘yan Najeriya da kada su yarda a hada lambarsu ta dan kasa da katin sim din wani daban, jaridar Punch ta rahoto.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Daraktan NCC, Efosa Idehen.
Da yake magana kan amfanin hada NIN da Sim, ya ce: “Kada wani dalili yasa kamfanin sadarwa ya bari wani mutum na daban yayi rijistar Sim da lambar NIN din wani."
A cewarsa, an bayar da wannan shawarar ne don kare ainahin mai lambar NIN din daga duk wasu matsaloli da zai taso daga amfani da SIM din wani.
Jaridar ta kuma nakalto yana cewa: "Idan mutanen, wadanda aka hada SIM dinsu da layinku, suna amfani da SIM dinsu don aikata laifi ko kowane irin ta'asa, cikin sauki za a gano shi zuwa gare ku, za a hukunta ku saboda SIM din yana da alaka da NIN din ku."
0 Response to "Lambar (NIN) tana matsayin Rayuwarka Ne Dolene Saika Kula Sosai Ncc Tayiwa 'Yan Najeriya Gargadi Mai Zafi Duba Abinda Tace>>>"
Post a Comment