Abubuwa guda takwas da Kanumfari keyiwa lafiyar Mata Da Maza Musamman Masu Aure
Kanunfari fitaccen sinadari ne da galibin mutane ke amfani da shi wajen girki da sha da kuma wasu abubuwan na inganta lafiya da jin daɗi.
Ana amfani da itacensa ko ganyensa ko busasshe a sarrafa su domin biyan bukatu daban-daban a ko ina a faɗin duniya. Ko da yake galibin Larabawa ko al'ummar yankin ƙasashen Asiya sun fi amfani da shi.
Sirrin shan ruwan kanumfari
Masana harkokin lafiya sun bayyana amfanin wannan sinadari na kanunfari a rayuwar dan adam.
A tattaunawarsa da BBC, wani likita a Najeriya Dr Ibrahim Badamasi, ya ce ruwan kanunfari na da amfani sosai ga lafiya saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke yaƙi da cututtuka da bunƙasa garkuwar jiki. Ruwan kanunfari na taimakawa wajen saurin narkewar abinci da hana cutar ulcer. Yana taimakawa lafiyar haƙora da hana kumburin dadashi da fitar da jini.
Sannan ruwan kanunfari na taimakawa wajen rage ƙiba da teɓa. Yana maganin jiri da cutar kwalara. Sannan yana taimakawa wajen saisaita sukari a cikin jini da lafiyar hanta saboda yana ƙunshe da sinadaran da ke hana lalata ƙwayoyin halita ga maza
Amfanin kanunfari ga mata
Amfanin kanunfari ga mata da maza kusan guda ne. Binciken da masana kimiyya da dama suka yi ya nuna cewa kanunfari na ƙara wa mata da maza ni'ima. Kanunfari na da amfani ga mata wajen inganta ƙwan haihuwa, sannan yana taimakawa wajen shawo kan matsalar rashin daukar ciki.
Kanunfari na bunƙasa isar wasu saƙonni ga ƙwaƙwalwa waɗanda ke motsa sha'awa ga mata da kuma maza. Kanunfari na ƙara wa mata kuzari lokacin jima'i. Baya ga taimakawa wajen rage jiki yana sa rashin tsufa.
Man kanunfari na taimaka wa mata wajen samun sauƙin ciwon mara a lokacin al'ada da taƙaita kwanakin al'adar.
Amfanin kanunfari ga maza
Kanunfari na ɗaya daga cikin magungunan gargajiya da ke ƙara wa maza lafiya domin kuwa yakan ƙara yawan sanadarin 'testosterone' wanda ke tasiri wajen haɓakar gaɓoɓin saduwa na namiji.
Rashin isasshen sanadarin 'testosterone' a jikin namiji na iya haifar masa da matsalar rashin ƙarfin mazakuta, wanda kan rage masa ƙarfin sha'awar saduwa.
Kanunfari kan inganta tafiyar maniyyin namiji. Yana kuma ɗauke da sanadarai da ke ƙara yawan maniyyin da namiji ke samarwa, wanda hakan shi ne abu mafi amfani ga lafiyar maza.
Bugu da ƙari kanunfari kan magance matsalar saurin fitar maniyyi ga namiji a lokacin saduwa, matsalar da ke yawan faruwa ga maza sanadiyyar gajiya ko kuma wasu matsaloli na daban.
Mai da ake samu daga kanunfari na ƙara ƙarfin miƙewar azzakari tare da inganta kwararar jini zuwa ga al'aura.
Ana amfani da kanunfari wajen magance saurin fitar maniyyi ga namiji a lokacin saduwa ne ta hanyar hada shi da wasu ƙarin abubuwan, wadanda akan shafa a kan al'aurar namiji kafin saduwa.
Ga dai jeren abubuwa 8 da kanunfari ke yi a jikin ɗan adam, daga Dr Badamasi
Yana kunshe da sindarai irin su Vitamin K da Fiber da Calories da carbs da Manganese
Yana kunshe da sindaran da ke hana lalata ƙwayoyin halitta
Yana iya taimakawa wajen hana kamuwa da kansa ko sankara
Yana kashe kwayoyin cutuka
Yana inganta lafiyar hanta
Yana daidaita sukari a cikin jini
Yana ƙara lafiyar ƙashi
Yana hana kamuwa da ulcer
Adadin kanunfari da za a iya sha a rana guda
Masana kiwon lafiya sun ce mutane na amfani da kanunfari wajen hana saurin fitar maniyyi a lokacin saduwa. Ko daɗin jima'i. Sai dai ba a son shansa ko ci ya zarta iyaka. Idan aka yi amfani da shi sama da ka'ida yana iya illa sosai.
Ba a son a sha sama da itace hudu zuwa biyar a kowacce rana. Sannan ya dangata daga mutum zuwa mutum. Amma yana da kyau a tuntuɓi likita domin samun shawarwari yadda ya kamata a yi amfani da shi.
0 Response to "Abubuwa guda takwas da Kanumfari keyiwa lafiyar Mata Da Maza Musamman Masu Aure"
Post a Comment