Wani abu daba kowane yasani ba gameda tarihin jarumi Sarki Ali Nuhu
Thursday, 19 August 2021
Comment
Ali Nuhu An haife shi a ranar 15 ga watan Maris shekara ta 1974 a Jihar Borno. Ya kasan ce Shahararren jarumin fina-finai, kuma mai shiryawa tare da bayar da umarni na fina-finan Hausa wato Kannywood da
Turanci a Najeriya wato Nollywood, Jarumin wanda ake ma lakani da Sarki musamman ma a masana'antar Kannywood, Shahararre ne a cikin dukkan jarumai na fina finai musamman na Hausa wato Kannywood, Sarki Ali Nuhu yayi aure ne shekarar ta 28/Disambar/2003.
Farkon rayuwa
An haifi Ali Nuhu a Maiduguri, jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya. Mahaifinsa Nuhu Poloma daga Balanga gari Jihar Gombe da mahaifiyarsa, da Fatima Karderam Digema daga Bama gidan gwamnatin jihar Borno. Ya girma a Jos da Kano.
Ilimi
Yayi karatu a Jami'ar Jos, Bayan karatun sakandare, ya sami digiri na farko a fannin ilimin fasaha daga Jami'ar Jos. Yayi bautar kasa a Ibadan da ke jihar Oyo. Daga baya ya halarci Jami'ar Kudancin Kalifoniya don yayi kwas a fagen shirya fina-finai da fasahar sinima.
fim
Ali Nuhu ya fara fitowa a fim ne a shekarar ta 1999 mai suna “Abin sirri ne”. An fi saninsa da rawar da yake takawa a "Sangaya" wanda ya zama ɗayan finafinan Hausa da suka fi samun kuɗi a lokacin. Ali Nuhu ya fito a fina-finai da dama, wadanda suka hada da Azal, Jarumin Maza, da Stinda a matsayin fitaccen Jarumi a wajen bayar da gudummawa a yayin bikin bayar da kyaututtuka na African Movie Academy a (2007). A shekarar ta 2019, Ali Nuhu ya yi bikin cikarsa shekaru 20 a masana'antar nishadantarwa. Ya fito a fina-finai kusan dari biyar (500).
Babban Jarumin Kannywood Ali Nuhu
Mabiya
inda akayi ittifaki akan yana da mabiya a Twitter sama da 140,000 da kuma mabiya a Facebook sama da 1,200,000 da kuma wasu a shafin Instagram sama da 1,000,000.
Fina finai a Kannywood
(BT) na nufin Ba Tabbas, ma'ana babu tabbacin kwanan wata da shekarar da fim din ya fita. Yayin da akwai wasu kuma da ake da tabbacin kwanan watan fitar su.
Kadan daga wasu Fina finai dayayi a masana'antar Kannywood
0 Response to "Wani abu daba kowane yasani ba gameda tarihin jarumi Sarki Ali Nuhu"
Post a Comment