--
Hukumar DSS na rike da fasfo din El- Zakzaky da maidakinsa,

Hukumar DSS na rike da fasfo din El- Zakzaky da maidakinsa,

>


Source: Punch (fassara)


Har yanzu shugaban Harkar Musulunci a Najeriya wato yan Shi'a, Sheikh  Ibraheem Zakzaky da maidakinsa Malama Zeenah ba su samu fita waje domin zuwa asibiti ba tun bayan da kotu ta wanke su ta kuma sallame su tsawon mako biyu da suka gabata, sakamakon riqe fasfo dinsu da jami'an tsaro su ka yi, kamar yadda JARIDAR PUNCH ta fahimta ranar Alhamis. 


A yayin taron manema labarai da Kungiyar mazauna Abuja ta shirya ranar Alhamis a Abuja kan lamarin, ta ce basu fasfo din su domin fita neman magani zai dawwamar da kwanciyar hankalin da garin ya samu tun bayan sakin su.


Shugaban kungiyar, Mista Danjuma Ayide, shi ne ya gabatar da takardar a wurin taron manema labaran mai taken 'Sakin Sheikh Zakzaky  ya yi daidai, an samu kwanciyar hankali a Abuja.'


A cewar sa, rahotanni sun bayyana rashin lafiyarsu na kara tabarbarewa wanda hakan ya sa su ke bukatar fita domin zuwa asibiti.


"Kungiyar mazauna Abuja ta yi farin ciki da hukuncin babbar kotu da ke Kaduna na ranar 28 ga Yuli, 2021.


"Sai dai, majiyarmu ta labarta mana cewar, bayan sakin su Sheikh Zakzaky din  da maidakinsa, sun zo Abuja da nufin fita waje domin neman magani, amman hakan ya gamu da cikas sakamakon rashin karbar fasfo dinsu da sauran kayayyaki.


"Muna kira ga gwamnati da ta taimaka don ganin an basu fasfo dinsu domin hakikar gaskiya muna fargabar sake wata zanga-zagar a Abuja.


"Muna shawartar shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya ba Sheikh Zakzaky da maidakinsa fasfo dinsu domin su fita zuwa asibitin da su ke bukata," a cikin takardar.


Source: Punchng

0 Response to "Hukumar DSS na rike da fasfo din El- Zakzaky da maidakinsa,"

Post a Comment