--
El-Zakzaky ya fallasa rashin tsoron Allah na mafi yawan kiristoci da musulman Nijeriya -Inji Reno Omokri

El-Zakzaky ya fallasa rashin tsoron Allah na mafi yawan kiristoci da musulman Nijeriya -Inji Reno Omokri

>


El-Zakzaky ya fallasa rashin tsoron Allah na mafi yawan kiristoci da musulman Nijeriya


Daga Reno Omokri

(Fassarar Ammar M. Rajab)


 

Yanzu ba labari bane cewa Ibraheem El-Zakzaky an sake shi tare da wanke shi da mai daraja mai shari’a Gideon Kurada ya yi, wanda hukuncinsa baki daya ya tabbatar da wanke jagoran ‘yan shi’a tare da bai wa ‘yan Nijeriya da yawa fata na cewa duk da mummunan kulli na wadannan mutanen biyu na Muhammadu Buhari da Nasir El-Rufai, za a iya samun adalci a Nijeriya.


An kama El-Zakzaky tare da tsare shi na tsawon shekaru shida. An kashe dubban magoya bayansa. Buhari ya kashe ‘ya’yan (Shaikh Zakzaky) shida. Sannan an rika farautar sauran mabiyansa. Amma duk da haka, ba su juya masa baya ba. Ina son yin nazarin rayuwar El-Zakzaky. {okarinsa na ci gaba da samun goyon baya abin a yaba ne. A na shi labarin, cikin littafin ‘The Beautiful Ones Are Not Yet Born,’, marubuci Ayi Kwei Armah, yana  cewa; “{yamar rashin adalci na haifar da neman adalci. Masu karatun da ba su ganin wannan alakar saboda burin kawai a nishadantar  da su, ba ni da wata basira ko fasahar sauya cutarwar mutane zuwa nishadi.”


Ban yadda da rashin adalcin da aka yi wa ‘yan shi’ar Nijeriya ba. Na samu gamsuwa da ya zama na yi magana a yayin da aka yi kisan kiyashin Zariya wanda aka kashe ‘yan shi’a akalla mutum 347 da ya hada  maza, mata, kananan yara da kuma jarirai (ba za a san ainihin adadin ba, amma tabbas ya zarce 347) wanda ya auku a tsakanin ranekun 12-15 ga watan Disambar 2015. Ba kawai na zama kirista na farko daga Kudanci bane wajen daukaka muryata wajen magana, na kuma kira tsohon shugaban kungiyar kiristoci ta Nijeriya (CAN), Fasto Ayo Oritsejafor, na roke shi da ya fitar da sanarwar goyon baya ga Harkar Musulunci a Nijeriya bisa zaluntarsu da Janaral Buhari ya yi musu. Na yi hakan ne ta hanyar gamsar da Fasto Ayo cewa da Kiristi (Annabi Isa) ya yi hakan tuni na abin da nake rokonsa ya yi.


Abin da ya faru na Disambar 2015 gwaji ne. Janaral Buhari ya gwada ‘yan Nijeriya domin ya ga gudun ruwansu na yadda za su yi hakuri da zaluncinsa. Da a ce mun dunkule wuri guda wajen yin Allah-wadai da abin da ya yi wa ‘yan shi’a, da bai ci gaba da aikata munanan ayyuka ba na kashe-kashen da ya ja ragama, wanda suka dawo da Nijeriya baya zuwa zamanin Abacha ba, ciki harda kisan kiyashin Lekki a yayin zanga-zangar #EndSARS, kisan kiyashin masu zanga-zangar lumana ta IPOB, da kuma kisan kare dangi na kabilanci da yake aukuwa yake kuma ci gaba da gudana a Kudancin Kaduna da Binuwe.


Kamar yadda na yi takaici, kuma har yanzu ina kullace da shugabannin kiristoci na Kudu, musamman bayan da Fasto Ayo ya kammala wa’adin mulkinsa a matsayin shugaban kungiyar Kiristocin Nijeriya, takaicina har wala yau, duk da ban yi mamaki ba, yana zuwa ne ga shugabannin Musulmin Arewa da suka amince, ta hanyar yin shiru, bisa ga abin da Janaral Buhari ya yi wa El-Zakzaky da ‘yan shi’a. A iya abin da zan iya tunawa, babu wata kungiyar Musulmi mai muhimmanci, harda karen farauta ma irin kungiyarnan ta Kudu (MURIC), da ta yi magana domin kare Harkar Musulunci a Nijeriya.


Na tuna yadda na kira wani fitaccen Musulmi dan Arewaci, kuma na tambaye shi dalilin da ya sanya al’ummar Musulmi ba su damu da makomar ‘yan Shi’a ba, sai ya gaya min cewa ba a yawan sha’awar musuluncin ‘yan Shi’a a Arewacin Nijeriya. Amma ko da hakan, shin ba su cancanci a ba su kariya saboda ƙimarsu ta asali a matsayin su na mutane ba?


Muna inda muke a yau a Nijeriya ne saboda; na daya, sun fara dirarwa ‘yan shi’a, amma bamu yi magana ba, saboda ni ba dan shi’a bane. Sai suka koma kan ‘yan IPOB, shima ban yi magana ba, saboda ni ba dan IPOB bane. Sai suka koma kan Sunday Igboho, shima ban yi magana ba, saboda ni ba mai goyon bayan kafa kasar Yarabawa bane. Sai suka dawo kaina, yanzu kuma babu wanda ya rage da zai yi magana a kaina. Wannan shi ne mafi yawan matsalolinmu a Nijeriya.


Wani lokacin ina zargin cewa abin da yake fuskantar kasarnan alhaki ne na abin da muka bari aka yi wa El-Zakzaky. Mutumin nan ya sha bakar wahala kafin ya samu ‘yancinsa, amma duk da haka bai karaya ba. A halin yanzu, Nijeriyar da ta so ta durkusar da shi, ita ke durkushewa, muna fatan ba har zuwa lokacin da ba za a iya gyarata ba. Ku mayar da hankalinku baya zuwa kan hoton El-Zakzaky cike da jini, ga harbin bindiga, idonsa daya ya kusan katsewa daga tushensa, yana kwance a gurgunce cikin baro (wheelbarrow), sojojin da Buhari da Buratai suka turo suka tafi da shi wurin da ba a sani ba. Kuma mene ne laifinsa? Wai mabiyansa sun tare babban hanya a Zariya, a yayin da tsohon shugaban rundunar Soja, Laftanar Janar Burutai (matsoracin da kawai yake da karfi idan yana fuskantar fararen hula marasa makami, amma ake nemansa a rasa a yayin da Boko Haram da ‘yan bindiga masu dauke da makami suka bayyana), ya zo garin wani taro. Kawai saboda wannan dalili mara hujja, gwamnatin Nijeriya suka aikata masa abin da ba su yi wa Boko Haram da ‘yan bindiga ba.


A karshen nazarina, El-Zakzaky ya fallasa rashin tsoron Allah na mafi yawan kiristoci da Musulman Nijeriya. Yawancin masu addini a Nijeriya suna son makwabtansu ne kamar yadda suke son kansu idan suna bin fahimtar addini iri daya. Sake karanta wannan kuma. Ba ina fadar abin da kuke tunanin ina fadi bane. Kiristocin Nijeriya ba lalai suna kaunar sauran kiristocin Nijeriya ba. Suna hakuri da su ne. Soyayayarsu sun tanade shi ne ga membobin darikarsu, kuma a wani lokacin ma, suna nuna matukar soyayyarsu ne kawai ga membobin cocinsu. Wannan haka yake ko gaskiya ne ga Musulmi ma.


Mun manta, ko watakila ba mu taba sani ba, cewa Ubangiji bai halicci mu a matsayin Yahudawa, Kiristoci, ko kuma Musulmai ba a rana ta shida. Abin da Ubangiji ya halitta a wannan rana mai albarka shi ne mutum. Addinin Ubangiji ba shi ne Yahudanci, Kiristanci, Musulunci ko kuma wani koyarwar addini ba. Addinin Ubangiji shi ne soyayya. Kuma irin wannan soyayyar ta Ubangiji ita ce soyayyar da na ga 'yan Shi'ar Nijeriya sun nuna wa Ibraheem El-Zakzaky. Ta hanyar wahalhalu, kashe-kashe, kuntatawa, wulakanci, wariya, da rugujewar tattalin arziki, 'yan Shi'ar Nijeriya suka tsaya kyam tare da Ibraheem El-Zakzaky.


Wannan kadai ya isa shaida cewa wannan mutumin (Zakzaky) yana da dabi’u na iya jagoranci fiye da yadda muke gani a Nijeriya a yau. Da a ce muna da jami’o’i da suka amsa sunansu, ya zuwa yanzu, da sun fara binciken mene ne, me yasa, da kuma yadda wannan mutumin El-Zakzaky ya iya gina irin wadannan dimbin mabiya, masu hadin kai, taimakon juna da kuma ‘yancin biyayya. Domin idan Nijeriya za ta fita daga kangin da Muhammadu  Buhari ya jefa ta a ciki harda gaba, muna da bukatar shugaba wanda zai iya ba da umurni ga wadannan mutane masu nuna soyayya, goyon baya, sadaukar da kai da biyayya.


Kuma a bayyane yake, ba ina magana akan irin goyon da aka gina shi akan mafarke-mafarke bane wanda ya sanya Yahuza Ibrahim daga Katsina ya sauya sunan’yarsa daga Buhariyya zuwa Kauthar, saboda, a cewarsa: “a baya, a lokacin da aka ambaci sunansa (Buhari), kowa ya dauka shi ne mutumin da ya dace, wanda zai taimaka wajen magance matsalolinmu. Amma sai ya juye ya zama akasin haka. Ina fada maka, shugaban kasar bai cika ko daya daga cikin alkawuran neman zabensa ba. Bai yi komai ba”. Babu wani dan shi’ar Nijeriya da zai fadi haka akan Ibraheem El-Zakzaky. Ko mutum daya!


Abin takaici, an daure Ibraheem El-Zakzaky a gidan yari na tsawon shekaru shida a mulkin zalunci na Buhari saboda laifin da bai aikata ba. A halin yanzu, ‘yan bindiga, makiyaya masu kisa, da Boko Haram har yanzu suna da ‘yanci bayan shekaru shida na mulkin Buhari na zalunci duk da dimbin laifukan da suka aikata. Kuma muna tunanin zaman lafiya a Nijeriya. Shin za a samu zaman lafiya a inda babu adalci?


An buga rubutun ne a shafinsa na ‘TheAlternative’, a Jaridar ThisDay ta ranar Larabar 4 ga watan Agustan, 2021.

0 Response to "El-Zakzaky ya fallasa rashin tsoron Allah na mafi yawan kiristoci da musulman Nijeriya -Inji Reno Omokri"

Post a Comment