--
An Haramta zancen dare ga Samari Da 'Yan Mata A jihar Kano,  Duba dalili

An Haramta zancen dare ga Samari Da 'Yan Mata A jihar Kano, Duba dalili

>
Hoto: Bar. Bulama Bukarti Source: Aminiya Daily Trusy



A Jihar Kano an haramta wa masoya haduwa a domin gudanar da zancen dare a karamar hukumar Rano ta jihar Kano, 


Dokar da aka kafa ta samo asali ne sakamakon rahotannin da ake samu na ayyukan lalata tsakanin 'yan mata da Samari maza. 


A cewar jami'in watsa labarai na karamar hukumar Rano, Habibu Faragai, shugaban majalisar, Dahiru Muhammad, ya sanar da dokar a wani taron kwamitin tsaro da mazauna yankin da shugabannin gargajiya suka halarta. 


Mista Muhammad ya ce kwamitin ya tayar da jijiyoyin wuya kan yawaitar lalata a karamar hukumar, 


Ya ce an sanya dokar ne don tsaftace yankin  na hana ayyukan lalata da ke faruwa yayin tattaunawar dare tsakanin Samari da 'Yan Mata A Yankin, 


Shugaban majalissar ya umarci hukumar Hisbah ta jihar da ('yan sandan) da sauran jami'an tsaro a matakin karamar hukuma dasu tabbatar da anbi dokar da kama masu aikata laifuka.

0 Response to "An Haramta zancen dare ga Samari Da 'Yan Mata A jihar Kano, Duba dalili"

Post a Comment