Zanbar Musulunci idan har Al-ummar Musulmi Basu taimakeni ba, -Cewar Wani Matashi Dan Jihar Jigawa
A wani rubutu da muka samo daga shafin yanar gizo na Facebook na Datti Assalaffiy, ya bayyana cewa akwai wani matashi da alamu suka nuna cewa ya fito daga jihar Jigawa wanda ke kokarin yin ridda ya fice daga addinin Musulunci.
Ya ce matashin mai suna Abba yana kokarin ficewa daga addinin Musulunci, saboda a cewar shi tunda ya taso babu wani amfani da addinin Musulunci ya kara masa.
Na bada kwanaki kadan a nuna mini alfanun Musulunci
Saurayin ya ce ya bada kwanaki kadan idan har al’ummar Musulmi ba su nuna masa wani abin amfani a cikin addinin Musulunci ba, haka kuma idan har gwamnatin Najeriya ba ta bashi babban mukami ba zai yi sallama da addinin Musulunci, kamar dai yadda ya bayyana hakan a wani bidiyo da ya sanya a shafinsa na Facebook.
Kamar yadda shafin na Datti Assalafiy ya wallafa, saurayin ana kyautata zaton ya fito daga jihar Jigawa.
Na karance Qur’ani baki daya banga wani amfaninsa ba
Kamar yadda saurayin ya bayyana, ya karance Al-Qur’aani mai girma baki data amma bai ci karo da inda ya kara masa amfanin komai ba sai tashin hankali.
A cewar Datti Assalafiy:
A maganganun yaron akwai yiwuwar dan kwangilar Yahudawa ne ko kuma yana da tabin hankali, ko kuma ya shiga addinin maguzawa na “Atheist”, wanda suke cewa babu Allah baki daya.
Amma ina kyautata zaton yana da tabin hankali, saboda ya ce dole sai gwamnati ta bashi mukami kafinn ya cigaba da zama a addinin Musulunci, wannan magana daa yayi tana kama da ta mutumin da ya samu matsalar kwakwalwa
Datti AssalafAssalafiy
0 Response to "Zanbar Musulunci idan har Al-ummar Musulmi Basu taimakeni ba, -Cewar Wani Matashi Dan Jihar Jigawa"
Post a Comment