--
Yanzu yanzu: Bayan haramta Bitcoin, CBN ta kirkiri amintattun kudaden Intanet na Najeriya

Yanzu yanzu: Bayan haramta Bitcoin, CBN ta kirkiri amintattun kudaden Intanet na Najeriya

>

Babban Bankin Najeriya ya ce zai kaddamar da tsarin gwajin kudinsa na intanet a ranar 1 ga Oktoba, 2021. A cewar Nairametrics, CBN tare da masu ruwa da tsaki sun bayyana kudirin su na kudin intanet a wata ganar yanar gizo mai zaman kanta wacce aka gudanar a ranar Alhamis, 22 ga watan Yulin 2021. 


A wani rahoto da jaridar Punch ta fitar kwanan nan, Gwamnan Babban Bankin na CBN, Godwin Emefiele ya sanar da cewa bankin na aikin samar da kudin na intanet a yayin taron Kwamitin Banki na 306. 


Nairametrics ta ce, majiyarta mai zaman kanta ta ce za a kaddamar da shirin ne a ranar 1 ga Oktoba, 2021. 


Ta ce a jawabin da Daraktan sahen IT, Rakiya Mohammed ta yi a karshen taron ta bayyana cewa Bankin ya kasance yana gudanar da bincike a game da kudaden intanet na babban bankin tun shekarar 2017 kuma hakon kan iya cimma ruwa kafin karshen wannan shekarar. 


Ana lakafta sunan aikin da Project GIANT kuma zai yi amfani da tsarin Blockchain na Hyperledger Fabric. 

0 Response to "Yanzu yanzu: Bayan haramta Bitcoin, CBN ta kirkiri amintattun kudaden Intanet na Najeriya"

Post a Comment