Rashida mai sa'a ta yi bayani dalla-dalla kan rade-radin aurenta da Iyan Tama duba abinda ta fada>>>
Jaruma Rashida Adamu Abdullahi ta musanta rade-radin dake yawo na cewa za ta angwance da Iyan-Tama
Kamar yadda ta sanar, ta ce fastar wani fim suka yi hotunan shine ta wallafa a shafinta na Instagram A cewarta, ta dauka furodusa Hamisu Lamido Iyan-Tama tamkar uba kuma akwai mutuntawa tsakaninsu
Sananniyar jarumar Kanyywoood, Rashida Adamu Abdullahi wacce ake kira da Mai Sa'a ta yi fatali da cece-kucen dake yawo ne cewa zata angwance tare da furodusa Hamisu Lamido Iyan-Tama.
Jama'a da yawa sun ta zaton aure manyan furodusoshin biyu za su yi bayan wasu hotunansu sun bayyana kuma jarumar ta wallafa a Instagram.
Sai dai jaruma Rashida ta zanta da Mujallar Fim inda ta tabbatar da cewa babu wani batun soyayya dake tsakaninta da babban furodusan, lamarin duk shiri ne.
Rashida ta ce tsakaninta da furodusa Iyan-Tama girmamawa ce kuma ta dauke shi tamkar mahaifinta. A cewarta, "Kowa ya san Iyan-Tama darakta ne, furodusa kuma jarumi ne a masana'antar
A gefe daya kuma uba ne. Tsakanina da Iyan-Tama kawai girmamawa da mutuntawa kwarai da gaske domin a yayin da yayi fina-finansa ban shigo industiri ba. "Jama'a suna ta cewa zan auri Iyan-Tama amma ba haka bane.
Fim din shi ne za a fitar wanda ya sha alwashin dawo da ni masana'antar a matsayin jaruma. Da farko na ce ba zan yi ba amma daga bisani na amince. Saboda haka muka yi wasu hotuna kuma za a saka a fastar fim din.
“Sunan fim din saura kiris kuma ko da na wallafa hotunan a shafina na Instagram na rubuta Saura Kiris."
0 Response to "Rashida mai sa'a ta yi bayani dalla-dalla kan rade-radin aurenta da Iyan Tama duba abinda ta fada>>>"
Post a Comment