--
Gwamnatin jihar Kano ta sanya sabuwar doka ga dalibai 'yan sakandire game da Lambar (NIN)

Gwamnatin jihar Kano ta sanya sabuwar doka ga dalibai 'yan sakandire game da Lambar (NIN)

>


Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa ya zama wajibi dukkan ɗaliban sakandiren jihar su yi rijista kuma su mallaki lambar zama ɗan kasa NIN, tun daga karamar sakandire JSS zuwa babba SS, kamar yadda dailytrust ta ruwaito. 


Kwamishinan ilimin jihar, Muhammad Sanusi Kiru, shine ya bada sanarwar yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Alhamis. 


Ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne domin gwamnati ta samu cikakken bayanan dalibai kuma hakan zai saukaka wajen yin kasafi da sauran lamarin da ya shafi dalibai. 


Kiru Ya ƙara da cewa idan ɗalibai suka yi rijista kuma suka mallaki NIN zamu samu damar samun bayanan halittarsu, zanen yatsu 10, karamin hoton ɗalibi, da kuma sanya hannun kowane ɗalibi. 


Hakazalika yace hakan zai taimaka wajen dakatar da yawan canza bayanan ɗalibai yayin jarabawa da kuma rage damar satar amsa a jarabawa 


Muna bukatar aiwatar da hakan nan take Kwamishinan ya yi kira ga shugabannin hukumar makarantu, (KSSMB), daraktoci, shugabannin sakandire da su tabbatar an aiwatar da wannan sabon umarni. 


Yace: "Ma'aikatar ilimi ta kammala duk wasu shirye-shirye tare da ofishin hukumar NIMC na jihar Kano game da yadda za'a yiwa ɗaliban rijistan a yankunansu." 

0 Response to "Gwamnatin jihar Kano ta sanya sabuwar doka ga dalibai 'yan sakandire game da Lambar (NIN)"

Post a Comment