--
Daga karshe: APC ta yanke hukuncin karshe kan Yari da Marafa,  Duba Abinda tace anan>>>

Daga karshe: APC ta yanke hukuncin karshe kan Yari da Marafa, Duba Abinda tace anan>>>

>


Legit.ng ta tattaro cewa shugaban rikon kwarya na jam'iyyar ta kasa, Gwamna Mai Mala Buni, ya rusa kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC a jihar tare da sanar da Matawalle a matsayin sabon shugaban jam'iyyar.


Kundin tsarin mulki ya daura jagorancin APC a Zamfara kan Gwamna Matawalle


Rahoton, ya ce Yari da Marafa sun ki amincewa da kaddamarwar da Buni yayi a hira daban-daban da suka yi da Sashen Hausa na BBC, suna masu cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa.


Da yake magana da jaridar kan batun a ranar Juma’a, 2 ga watan Yuli, sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata John Akpanudoedehe, ya ce Gwamna Buni ya fadi zuciyar jam’iyyar, yana mai cewa ba batun rikici ba ne.


Ya ce:


“Na daidaita kaina da shugabanmu na kasa, Gwamna Mai Mala Buni. Ya yi magana da tunanin jam’iyya; wannan ba batun rikici baneMarafa



Daily Trust ta ruwaito Sanata Ahmed Yerima, tsohon gwamnan jihar, ya ce kamar yadda abubuwa suka tsaya a jihar Zamfara, Matawalle shine shugaban dukkan mambobin jam'iyyar APC.


Yerima ya ce:


“Ga kowane dan jam’iyyar APC a Zamfara yanzu, ko ya fada ko bai fada ba, kundin tsarin mulki ya ba Bello Matawale shugabancin APC. Saboda haka, dukkanmu muna karkashin jagorancin gwamnan jihar Zamfara na yanzu."


Jigon APC a Zamfara ya yi kira da a kori tsohon Gwamna Yari da Marafa


A wani labarin, wani jigon jam'iyyar All Progressive Congress, APC, a jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi ya nuna bacin ransa game da matakin da tsohon gwamna Abdul'azeez Yari da Sanata Kabiru Marafa suka dauka kwanan nan game da shawarar kwamitin rikon jam'iyyar na kasa.


Shugabannin jam'iyyar na kasa a lokacin sauya shekar gwamna Bello Matawalle da sauran mambobin jam'iyyar sun rusa majalisar zartarwar APC a Zamfara tare da ayyana gwamnan a matsayin shugaban jam'iyyar a jihar.


Shinkafi a wani taron manema labarai a Gusau, babban birnin jihar a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli, ya yi kira ga jam’iyyar ta kasa da ta yi maganin duk wanda ya karya dokar APC a Zamfara.


Source: Legit.ng

0 Response to "Daga karshe: APC ta yanke hukuncin karshe kan Yari da Marafa, Duba Abinda tace anan>>>"

Post a Comment