Da duminsa: Kotu ta tilasta Ganduje biyan tarar dubu N800,000 Duba Dalili>>>
Tuesday, 6 July 2021
Comment
Babbar Kotun jihar Kano a yau Talata ta ci tarar Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano N800,000 bayan ya janye ƙarar da ya shigar da jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar kan zargin bata masa suna.
A makon jiya ne Gwamna Abdullahi Ganduje ya shigar da Jaafar karar kan wasu faya-fayan bidiyo da jaridarsa ta wallafa inda aka ga Gwamnan yana zuba Daloli a aljihunsa, wadanda ake zargin na cin hanci ne.
Jaridar Aminiya ta ruwaito da yake yanke hukunci a kan buƙatar Jaafar na a biya shi da jaridarsa Naira miliyan 400 saboda bata masa lokaci, alƙalin kotun, Mai Shari’a Suleiman Danmalam ya umarci Ganduje ya biya tarar saboda janye ƙarar ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba.
Mawallafin jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar wanda a yanzu haka yana gudun hijira a ƙasar Birtaniya, ya bayyana murnarsa da hukuncin kotun na yau, inda ya rubuta shafinsa na Facebook “Alhamdulillah” ma’ana godiya ta tabbata ga Allah.
Source: Hausa Daily Times
0 Response to "Da duminsa: Kotu ta tilasta Ganduje biyan tarar dubu N800,000 Duba Dalili>>>"
Post a Comment